Hotunan yadda Amurkawa ke fama da tsananin zafi

An wallafa

An gargadi sama da mutum miliyan tara ne a faɗin jihohi tara da ke arewaci da tsakiyar Amurka kan tsananin zafi a ranar Litinin - ana sa ran wannan adadin zai ƙaru nan da kwanaki masu zuwa.

A makonni masu zuwa, kusan kashi 70 cikin 100 na Amurkawa za su yi rayuwa a cikin tsananin zafi wanda zai iya kaiwa maki 32 a ma'aunin selshiyos, haka kuma kusan kashi 20 na ƙasar za su yi rayuwa a yanayin zafi na sama da maki 37 a ma'aunin selshiyos.

Tsananin zafi ya fi kashe Amurkawa fiye da duk wani sauyin yanayi a duk shekara.

An ƙiyasta cewa aƙalla mutum 138 ke mutuwa a duk shekara a Amurka sakamakon tsananin zafi tun daga 1990 zuwa 2019, kamar yadda hukumar da ke kula da hasashen yanayi ta Amurka ta bayyana.

Yvette Johnson mai shekara 54 kenan a yayin da take zaune a waje tana shan fanka a ranar 10 ga watan Yunin 2022 a Houston da ke Jihar Texas ta Amurka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yvette Johnson mai shekara 54 kenan a yayin da take zaune a waje tana shan fanka a ranar 10 ga watan Yunin 2022 a Houston da ke Jihar Texas ta Amurka
1px transparent line
Manyan motoci a Amurka yayin da suke barin mutane na shiga kyauta, suna ba fasinjoji dama su sha iska sakamakon irin zafin da ake fama da shi a Austin da ke Texas.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Manyan motoci a Amurka yayin da suke barin mutane na shiga kyauta, suna ba fasinjoji dama su sha iska sakamakon irin zafin da ake fama da shi a Austin da ke Texas.
1px transparent line
Mahalarta wani biki na waƙoƙi da kimiyya na Bonnaroo a yayin da suka tsaya a tsaye kusa da wata ƙatuwar fanka inda suke shan iska sakamakon zafin da ake yi a birnin Manchester da ke Jihar Tennessee ta Amurka.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mahalarta wani biki na waƙoƙi da kimiyya na Bonnaroo a yayin da suka tsaya a tsaye kusa da wata ƙatuwar fanka inda suke shan iska sakamakon zafin da ake yi a birnin Manchester da ke Jihar Tennessee ta Amurka.
1px transparent line
Masu kashe gobara kenan a yayin da suke ƙoƙarin kashe wata wutar daji da ta kama a ranar Juma'a, 17 ga watan Yunin 2022 a Jurupa Valley da ke Jihar California ta Amurka

Asalin hoton, VCG via Getty Images

Bayanan hoto, Masu kashe gobara kenan a yayin da suke ƙoƙarin kashe wata wutar daji da ta kama a ranar Juma'a, 17 ga watan Yunin 2022 a kwarin Jurupa da ke Jihar California ta Amurka

Duka waɗannan hotunan suna da hakkin mallaka