Hotunan yadda Amurkawa ke fama da tsananin zafi

An wallafa

An gargadi sama da mutum miliyan tara ne a faɗin jihohi tara da ke arewaci da tsakiyar Amurka kan tsananin zafi a ranar Litinin - ana sa ran wannan adadin zai ƙaru nan da kwanaki masu zuwa.

A makonni masu zuwa, kusan kashi 70 cikin 100 na Amurkawa za su yi rayuwa a cikin tsananin zafi wanda zai iya kaiwa maki 32 a ma'aunin selshiyos, haka kuma kusan kashi 20 na ƙasar za su yi rayuwa a yanayin zafi na sama da maki 37 a ma'aunin selshiyos.

Tsananin zafi ya fi kashe Amurkawa fiye da duk wani sauyin yanayi a duk shekara.

An ƙiyasta cewa aƙalla mutum 138 ke mutuwa a duk shekara a Amurka sakamakon tsananin zafi tun daga 1990 zuwa 2019, kamar yadda hukumar da ke kula da hasashen yanayi ta Amurka ta bayyana.

Duka waɗannan hotunan suna da hakkin mallaka