Ku San malamanku tare da Sheikh Sa'id Haruna Hassan, mai jan baƙin Sheikh Ja'afar
Sheikh Sa'id Haruna Hassan, wanda ya girma a birnin Kano da ke arewacin Najeriya, ya bayyana cewa ya yi karance-karancensa ne a tsakanin Kano da Maiduguri da ke arewa maso gabas.
Ya bayyana haka ne a shirnmu na Ku San Malamanku.
Malamin ya bayyana cewa haduwarsa da fotaccen malamin nan marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam ta yi matukar tasiri ga rayuwarsa ta neman ilimi.
"Allah Ya saka wa Malam Ja'afar da alheri, da iyayensa da shi Allah Ya lullube su da Rahamarsa," in ji Malamin.
"Dama ni tunda na taso ni mutum ne mai son ya yi karatu irin na Larabawa.
" To asalin haduwar mu da Sheikh Ja'afar sai ya bude makaranta da ake kira 'Ihya'ul-Sunnah a anguwar Tsohuwar Sheshe da ke cikin birnin Kano."
A cewar Malamin a nan ne ya fara koyon 'Huruf', har ya zamto cewa sun saba sosai da marigayi Sheikh Ja'afar.
A kan haka ya ce ba a ma taba yi masa mutuwar da ta girgiza shi ba kamar ta Malam Ja'afar.
Sheikh Sa'id Haruna ya ce ya fara jin ana yada jita jitar cewa an kashe Sheikh Ja'afar amma dai bai yi saurin gaskata batun ba duk da jikinsa ya yi sanyi a lokacin.
"Daga nan sai wani ya kira ni daga Tudun Murtala sai ya ce Malam Abdullahi Pakistan ya fada maka cewa an kashe Malam Ja'afar yanzu ma yana gaban gawarsa."
Daga nan, a cewar Malamin, bai san lokacin da ya kai kansa Dorayi ba.
Ya kara da cewa marigayin ne ya koya masa tsoron Allah da tausayi da kyauta da kuma jarumta, don mutum ne da ba shi da tsoro.
Sheikh Sa'id Haruna ya kuma ce babu wani abu da yake so ya ga yana yi kamar karanta Al-Kur'ani.
"Duk ranar da na wuni ban karanta Al-Kur'ani ba, ba na jin dadi. Ba ni da wani abu da yafi wannan muhimmanci a rayuwata", a cewar Malamin.
Sannan ya ce ba shi da wani buri da ya wuce ya ga cewa ya gama da duniya lafiya.
Wani abu game da malamin shi ne 'ya'yansa da dama sun mutu, don a cewarsa 'ya'yansa 17 ne suka rasu, amma yanzu yana da 20, sannan matansa uku.










