Ku San Malamanku tare da Malama Habiba Yahya, matar Farfesa Maqri

Bayanan bidiyo, Bidiyon Ku San Malamanku tare da Malama Habiba Yahya, matar Farfesa Maqri
An wallafa

Malama Dr Habiba Yahya Alfadarai, matar Farfesa Sheikh Ibrahim Maqari, ta ce ta yi saukar Al-Ƙur'ani mai girma tana 'yar shekara 12 da haihuwa a hannun iyayenta.

Malamar da ta yi digiri uku a harshen Larabci, ta faɗa wa BBC Hausa hakan ne cikin Shirin Ku San Malamanku da muke wallafawa duk ranar Juma'a.

An haifi Dr Habiba a unguwar Alfadarai da ke cikin birnin Zariya na Jihar Kaduna a arewacin Najeriya.

Yanzu haka malamar babbar jami'a ce a hukumar kula da ilimin Arabiyya da Musulunci ta Najeriya wato National Board for Arabic and Islamic Studies (NBAIS).

Neman ilimi da kuma aiki sun kai ta jihohi daban-daban a Najeriya da suka haɗa da Kano da Kogi.

Neman ilimi

Dr Habiba ta fara karatun firamare a ɓangaren mata na makarantar Jama'atu a shekarar 1993.

Daga baya kuma ta koma Kano, inda ta shiga sakandaren mata ta GGASS Ɗan Zabuwa, kuma ta kammala a 1999.

A shekarar dai ta samu gurbin karatu a Jami'ar Ahmadu Bello da Zaria (ABU) har zuwa 2004, inda ta samu shaidar digirin farko a harshen Larabci.

A 2005 ta sake samun gurbin digiri na biyu a ABU har zuwa 2009. Ta yi digirinta na uku a Jami'ar Jihar Kogi a 2015.

Ilimin addini

Bayan ta sauke Al-Ƙur'ani tana shekara 12, malamar ta ci gaba da maimaitawa har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, kamar yadda ta bayyana.

Dr Habiba ta ce babban malaminta shi ne mijinta Farfesa Maqari.

"Da yawa daga cikin karatun addini da ma bokon, kusan duka ta hannunsa na yi," in ji ta.

"Akwai malamin da na yi karatun addini a hannunsa mai suna Malam Haruna, wanda maƙwabci ne kuma kamar mahaifi yake ga iyayena.

"Akwai wani Malam Nafi'u, shi ma na yi karatun zaure a hannunsa."

Ƙwarewa

Dr Habiba ta ƙware ne a ɓangaren adabi ko kuma rubutun zube na harshen Larabci.

Kazalika, ta fi mayar da hankali kan rubutawa da shirya wasannin kwaikwayo da kuma rubutun ƙagaggun labarai.

Malama Habiba kan shirya karatun tafsiri na mata zalla da sauran laccoci.

Presentational grey line

Ƙarin labarai