Palm Sunday: Kiristoci na bikin tunawa da shigar Yesu birnin Ƙudus

An wallafa

A ranar Lahadi 10 ga watan Afrilu Kiristoci a faɗin duniya ke bikin Palm Sunday - wadda ka iya nufin Lahadin Kwakwa da Hausa.

Bikin na nuna ranar ƙarshe ta makon Lent, inda mabiya adinin Kirista ke haƙura ko kuma su daina aikata abubuwan da suka fi so na tsawon kwana 40.

VATICAN CITY, VATICAN - APRIL 10: Pope Francis attends the Sunday Palm Mass at St. Peter's Square on April 10, 2022 in Vatican City, Vatican. Palm Sunday is a Christian moveable feast that falls on the Sunday before Easter, and marks the start of Holy Week. (Photo by Franco Origlia/Getty Images)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fafaroma Francis kenan a Dandalin St. Peters da ke Fadar Vatican ranar Lahadi 10 ga watan Afrilu yayin da gana da mabiya ɗariƙar Katolika

Palm Sunday rana ta musamman ga Kiristoci. Alama ce ta shiga Mako Mai Tsarki kuma kodayaushe bikin na faɗowa ne a kowace Lahadi wadda daga ita sai bikin Ista (Good Friday da Easter Sunday).

VATICAN, VATICAN CITY, APRIL 10: Pope Francis greets the faithful at the end of the Palm Sunday Mass in St. PeterÃs square at the Vatican City Vatican, on April 10, 2022. After 2 years of Covid-19 pandemic restrictions the Pope returns to lead outdoor crowded celebrations. (Photo by Isabella Bonotto/Anadolu Agency via Getty Images)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mabiya kenan a Fadar Vatican lokacin da Fafaroma Francis ke gaishe su karon farko cikin shekara biyu sakamakon annobar korona

Ana bikin Palm Sunday ne don tunawa da lokacin da Yesu Almasihu ya shiga Birnin Ƙudus 'yan kwanaki kafin ya bar duniya.

Palm Sunday procession from Maroun Church in downtown Beirut on April 10, 2022. (Photo by Fadel Itani/NurPhoto via Getty Images)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mutum kenan tare da wani ƙarin yaro yayin bikin Palm Sunday a Beirut babban birnin Lebanon

Littafi Mai Tsarki na Bible da Kiristoci suka yi imani da shi, ya ce Yesu ya shiga Birnin Ƙudus a kan jaki, inda mutane suka dinga ɗaga masa ganyen kwakwa don nuna murnarsu.

Palm Sunday procession from Maroun Church in downtown Beirut on April 10, 2022. (Photo by Fadel Itani/NurPhoto via Getty Images)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mazauna Beirut kenan na Cocin Maroun suke biikin Palm Sunday ranar 10 ga watan Afrilu

Akwai abubuwa da dama da Kiristoci ke yi a bikin na wannan rana.

Christian devotees take part in the Palm Sunday procession in Amritsar on April 10, 2022. (Photo by Narinder NANU / AFP) (Photo by NARINDER NANU/AFP via Getty Images)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kiristoci masu ibada na gudanar da tattaki na bikin Palm Sunday a Amritsar, Indiya

Ɗaya daga cikin abubuwan da aka fi yi shi ne bai wa masu ibada ƙananan ganyayyaki na bishiyar kwakwa.

Christian devotees take part in the Palm Sunday procession in Pondicherry on April 10, 2022. (Photo by Arun SANKAR / AFP) (Photo by ARUN SANKAR/AFP via Getty Images)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Indiyawa Kiristoci kenan suke tattaki a Pondicherry

Hakan na nufin tunawa da zuwan Yesu Ƙudus da kuma barinsa duniya 'yan kwanaki bayan haka.

Roman Catholic nuns carry palm branches as they circle the aedicule during the Palm Sunday procession at the Church of the Holy Sepulchre in Jerusalem's Old City, on April 10, 2022. - The ceremony is a landmark in the Roman Catholic calendar, marking the triumphant return of Christ to Jerusalem the week before his death, when a cheering crowd greeted him waving palm leaves. Palm Sunday marks the start of the most solemn week in the Christian calendar. (Photo by AHMAD GHARABLI / AFP) (Photo by AHMAD GHARABLI/AFP via Getty Images)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu mata kenan riƙe da rassan bishiyar kwakwa yayin tattakin Palm Sunday a Birnin Ƙudus na Isra'ila

Wasu Kiristocin kan ajiye kuros ɗinsu a gida, wasu kan ƙona shi kuma su ajiye tokar don su yi amfani da ita a bikin Ash Wednesday na shekara mai zuwa.

LIPNICA MUROWANA, POLAND - APRIL 10: Handmade palms surround the St. Szymon's monument during the 63rd edition of Lipnica Palms and Artistic Handicraft Competition during the Palm Sunday on April 10, 2022 in Lipnica Murowana, Poland. Palm Sunday is a Christian moveable feast that falls on the Sunday before Easter, and marks the start of Holy Week. (Photo by Omar Marques/Getty Images)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ganyayyakin bishiyar kwakwa kenan da aka ƙera da hannu da aka zagaye ginin St. Szymon yayin wata gasa da aka saka don bikin Palm Sunday a Lipnica Murowana da ke ƙasar Poland

Kazalika, Palm Sunday na bai wa Kiristoci damar tunawa da rayuwar Yesu a makon ƙarshe kafin su gudanar bukukuwan Ista.

Dukkan hutunan na da haƙƙin mallaka.