Palm Sunday: Kiristoci na bikin tunawa da shigar Yesu birnin Ƙudus

An wallafa

A ranar Lahadi 10 ga watan Afrilu Kiristoci a faɗin duniya ke bikin Palm Sunday - wadda ka iya nufin Lahadin Kwakwa da Hausa.

Bikin na nuna ranar ƙarshe ta makon Lent, inda mabiya adinin Kirista ke haƙura ko kuma su daina aikata abubuwan da suka fi so na tsawon kwana 40.

Palm Sunday rana ta musamman ga Kiristoci. Alama ce ta shiga Mako Mai Tsarki kuma kodayaushe bikin na faɗowa ne a kowace Lahadi wadda daga ita sai bikin Ista (Good Friday da Easter Sunday).

Ana bikin Palm Sunday ne don tunawa da lokacin da Yesu Almasihu ya shiga Birnin Ƙudus 'yan kwanaki kafin ya bar duniya.

Littafi Mai Tsarki na Bible da Kiristoci suka yi imani da shi, ya ce Yesu ya shiga Birnin Ƙudus a kan jaki, inda mutane suka dinga ɗaga masa ganyen kwakwa don nuna murnarsu.

Akwai abubuwa da dama da Kiristoci ke yi a bikin na wannan rana.

Ɗaya daga cikin abubuwan da aka fi yi shi ne bai wa masu ibada ƙananan ganyayyaki na bishiyar kwakwa.

Hakan na nufin tunawa da zuwan Yesu Ƙudus da kuma barinsa duniya 'yan kwanaki bayan haka.

Wasu Kiristocin kan ajiye kuros ɗinsu a gida, wasu kan ƙona shi kuma su ajiye tokar don su yi amfani da ita a bikin Ash Wednesday na shekara mai zuwa.

Kazalika, Palm Sunday na bai wa Kiristoci damar tunawa da rayuwar Yesu a makon ƙarshe kafin su gudanar bukukuwan Ista.

Dukkan hutunan na da haƙƙin mallaka.