An kashe sojojin Mali takwas, biyar sun bata bayan Faransa ta sanar da janye dakarunta

Asalin hoton, AFP
Rundunar sojin Mali ta ce an kashe sojojinta takwas sannan biyar sun ɓata bayan wani hari da 'yan tawaye suka kai a arewa maso gabashin kasar.
Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan da Faransa da ƙawayenta suka ce za su janye dakarunsu daga Mali, inda suka kwashe kusan shekara goma suna yakar masu da'awar jihadi.
Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce, sojojin saman Mali sun kashe mayaka kusan 60.
Rundunar ta ce sojojin na neman maboyar 'yan tawaye ne a lokacin da suka yi ta luguden wuta a yankin Archam.
An ta samun fargaba a yankunan ƙasar da ma ƙetare kan batun tsaro sakamakon korar dakarun Faransa da kuma yadda sojojin hayar Rasha suka samu gindin zama a ƙasar.
A wannan makon kaɗai, mazauna ƙasar sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an kashe farar hula 40 a yankin na Archam wanda yanki ne da ƙungiyar IS da sauran ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi ke kai hare-hare.
Mali ta shafe tsawon shekaru tana fama da masu iƙirarin jihadi, lamarin da ya jawo babbar zanga-zanga a 2020 inda jama'ar ƙasar suka rinƙa adawa da shugaban ƙasar na lokacin Ibrahim Boubacar Keita wanda aka hamɓarar da gwamnatinsa ta hanyar juyin mulki.
Tun bayan nan, sabbin shugabannin sojin ƙasar sun ta samun rashin jituwa da ƙasar Faransa inda har sojojin suka saɓa alƙwarinsu na ƙin gudanar da zaɓe a bana da kuma korar jakadan Faransa a lokacin da ya nuna turjiya kan lamarin.
Lamarin Mali ya yi ƙamari inda har ta buƙaci Faransa ta janye dakarunta bayan kusan shekara goma suna taya su yaƙar masu iƙirarin jihadi.
Da taimakon sauran sojojin wasu ƙasashen yammacin nahiyar, rundunar haɗaka ta Mali wadda ake kira Takuba Task Force za ta ƙara matsawa gaba kaɗan zuwa iyaka da Nijar .
Shugaban Nijar a ranar Juma'a ya bayyana cewa akwai yiwuwar iyakokin ƙasar za su zama cikin barazana bayan janyewar dakarun Faransa da ƙawayensu daga Mali.
Ko a farkon makon nan, sai da shugaban na Nijar da wasu shugabannin ƙasashen Yammacin Afrika suka haɗu da Shugaba Emmanuel Macron gabannin sanar da batun janyewar sojojin Faransa daga Mali inda a wurin ne suka amince da cewa dakarun za su koma wasu yankunan ƙasashen.











