Abin da ya sa sojojin Faransa suka bar Mali da abin da zai samu nahiyar bayan haka

Asalin hoton, AFP
Shugaba Emmanuel Macron ya sanar da cewa zai janye dakarun Faransa daga kasar Mali, inda suke fafatawa da mayaka masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama tun a shekarar 2013.
Akwai dakarun Faransa 5,000 a kasar ta Mali da kuma kasashen da ke kewaye da ita, suna fafatawa da kungiyoyi kamar su -Qaeda da kuma IS.
Amma a cikin sama da shekaru takwas, kasancewar Faransa ya kara rashin tagomashi a tsakanin gwamnati da 'yan kasar.
Wace irin barazana 'yan ta'adda ke yi wa kasar Mali da yankin Sahel?
Duka kungiyoyin IS da na al-Qaeda sun yanke shawarar mayar da hankulasu kan yankin Sahel na Afirka, bayan da aka gasa musu aya a hannu a yankin Gabas ta Tsakiya.
Sahel zirin yanki ne mai yanay da ke karkashin Hamadar Sahara da ya mike zuwa fadin nahiya daga- gabashi -zuwa -yammaci. Ya hada da bangaren kasashen Chadi,da Nijar, da Mali, da Burkina Faso da kuma Mauritania.
Kungiyar Kasar Musulunci da ke yankin Sahara (ISGS) da kuma bangaren kungiyar al-Qaeda da ake kira Jamaat Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), sun kai hare -haren ta'addanci a yankin wanda ya hallaka dubban mutane, tare da haddasa rasa matsugunan sauran daruruwan mutane, da kuma rufe makarantu.
Akwai sauran kungiyoyin masu jihadi biyu da ke cigaba da kai hare-hare a yankin na Sahel: Ansaroul Islam da Boko Haram.
Me yasa Faransa ta shigo ciki?
A shekarar 2013, Faransa ta aike da dakaru 5,000 zuwa kasar Mali a bisa amincewar gwamnati saboda suna fuskantar hare-haren 'yan tawaye masu rike da makamai.
Bayan hambararwa tare da kashe shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi, Buzaye sojojin hayar da suka dade suna taya shi yakin suka koma gida Mali tare da jajircewa kan neman 'yancin cin gashin kan arewacin kasar.
Tare da yin amfani da makaman Gaddafi, sun hada kawance da kungiyar da ke da alaka da al-Qaeda. Sun kuma karbe ikon arewacin tare da barazanar karbe ikon daukacin kasar.
Faransa ce ta mulki kasar Mali har ya zuwa shekarar 1960. Gwamnatin kasar Faransa ta ce tana bukatar ganin ta kare al'ummar kasar Mali da kuma 'yan kasar Faransar 6,000 da ke zaune a can.

Asalin hoton, Getty Images
Daga cikin wadancan dakaru, an kai 2,400 zuwa arewacin Mali; sauran kuma sun rika amfani da jiarge marasa matuka da jirage masu saukar angulu wajen farautar sansanonin mayaka masu jihadin da ke kai hare-hare a yankin Sahel.
Akwai kuma dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya 14,000 da ke aiki tare da dakarun gwamnati, suna sintiri a fadin hamadar yankin Sahel.
Me yasa zaman Faransa ya kasance babu sauran tagomashi?
Lokacin da dakarun Faransa suka isa kasar Mali a karon farko shekaru tara da suka gabata, sun samu kyakkawar tarba, amma tuni angantakar ta yi tsami.
Adadin kai hare-hare a kasar sun karu matuka, haka ma yawan 'yan kasar Mali da ke shiga kungiyoyin masu tayar da kayar baya.
A cikin shekaru tara da suka gabata, barazanar hare -haren mayaka masu tsattsuaran ra'ayin addinin Islama ya kuma bazu zuwa sauran kasashe kamar su Burkina Faso da Nijar, inda wasu mau tayar da kayar bayan ke kai samame a yankin daga sansanoninsu a cikin Hamadar Sahara.
Mazauna yankin da dana da ganin cewa kamata ya yi Faransa a matsayinta na kasar da ta cigaba a karfin soji, a ce ta iya shawo kan matsalar ta'addanci kana cewa ta fice daga kasar idan ba za ta iya ba.
Wasu sun yi kiran zaman dakarun kasar da ta mulke su, a matsayin ''kama-wuri-zauna''

Asalin hoton, Getty Images
Akwai kuma kace-nace tsakanin gwamnatin Faransa da tawagar sojin ta ta karbe mulki a watan Agustar shekarar 2020 - karo na biyu da aka hambarar da gwamnatin farar hula a cikin shekaru takwas.
Rundunar sojin ta sake dawowa da yarjejeniyar gudanar da zabuka a cikin wannan wat ana Fabrairu kana ta ce za ta cigaba da mulki har ya zuwa shekarar 2025.
A lokacin da Jakanadan kasar Faransa yan una adawa da hakan ne aka kore shi.
Shugaba Macron ya ce: "Ba za mu cigaba da kasancewa cikin aikin soji tare da haramtattun hukumomin da tunani da tsarinmu ba iri daya ba.
Faransa ta ki ta amince da zaman tattaunawar zaman lafiya da kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama, wanda manufa ce da 'yan kasar Mali da dama ke goyon baya.
Faransar ta kuma nuna fushinta kan matakin sojojin juyin mulki na gayyatar sojojin haya daga kamfanin Wagner na kasar Russia, don taimakawa wajen yaki da kungiyoyi masu jihadi.
Minsitar harkokin sojin kasar Faransa Florence Parly ta bayyana cewa ''za za mu iya mu'amala da sojojin haka ba''.
Me zai faru yanzu?
Za a janye dakarun kasar Faransa da ke aiki a rundunar Operation Barkhane nan da watanni hudu masu zuwa.
Faransa za ta aike da dakaru a sauran kasahen yankin Sahel, tare da dakarun sauran kasashen Turai, da ke aiki da rundunar Takuba.
Kasashen da ke cikin tafiyar sun ce za su bullo da tsare-tsare kan yadda za su rika aiki a yankin na gaba.
Gwamnatocin kasashe makwabta sun damu matuka cewa janyewar Faransa daga kasar Mali ka iya haifar da karin tashen-tashen hankula a yankin.
Shugaban kasar Ivory Coast Alassane Ouattara ya yi gargadin cewa hakan zai haifar da gibin siyasa.
"Zai zama wajibi mu kara yawan dakarunmu, tare da kara kare kan iyakokinmuu, ya ce.
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta bar dakarunta na wanzar da zaman lafiya a cikin kasar Mali duk kuwa da ficewar kasar Faransa.
Wasu 'yan kasar Mali sun yi lale marhabun da zuwan rundunar sojojin haya na kamfanin Wagner, da suke kallonta a matsayin 'yan ba ruwanmu.
Amma kuma, kasashen Yammaci da dama sun nuna rashin yarda da ita, kana sun zargi gwamnatin kasar Russia da taimaka mata cin galabar aikinta a kasar ta Mali.
Kamfani Wagner ya dade yana gudanar da aiki a sauran kasashen Afirka da dama, da suka hada da Mozambique, da Sudan da Jamhuriyra Tsakiyar Afirka.
Ana kuma danganta ta da aikata laifukan yaki a yakin basasar kasar Libya.











