Ku San Malamanku tare da Sheikh Adamu Muhammad Dokoro

Bayanan bidiyo, Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Adamu Dokoro
An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

An haifi Sheikh Adamu Muhammad Dokoro a Unguwar Bolari da ke garin Gombe a arewa maso gabashin Najeriya.

Malamin ya ce ba shi da tabbaci a kan ranar haihuwarsa sai dai kwatance amma an rubuta masa cewa an haife shi ranar 15 ga watan Mayun 1964.

Sheikh Dokoro bai girma a cikin gidansu ba, domin tun yana ɗan shekara uku zuwa huɗu sai aka kai shi makaranta ƙauye.

Ya yi karatu a gaban malaminsa wato Malam Isma'il. Ya ce Malam Isma'il ya ga karatun ɗalibinsa Adamu Muhammad Allah ya sa albarka a ciki sakamakon cikin rukunin almajiran da ke a gabansa babu wanda ya samu fatahi da buɗi irinsa.

Hakan ne ya sa Malam Isma'il ya dauke shi ya kai shi wajen wani alaramma wanda ake kira Malam Audu Mai Darasu, wanda ya kasance gangaran ne a lokacin.

Sheikh Adamu ya ce ya samu karɓuwa a wajen malamin sosai wanda ko yankar farce za a yi wa Malam Audu, Sheikh Adamu ne ke yi masa inda sauran gardawa da malamai suna zaune domin babu wanda ya samu kusanci da shi kamar yadda ya samu.

"Na zauna a wannan tsangaya ɗin ta kai shekara kusan 15 ko ma 16, Allah ya bada karatun Al-Ƙur'ani kuma an yi shi kuma zan iya cewa kafin na bar wurin, mafi rinjaye a cikin kwana shida zan rubuta Al-Ƙur'ani a wannan lokaci domin duk rana idan na tashi zan iya rubuta izu goma," in ji Sheikh Adamu.

Sheikh Adamu ya ce da ya dawo cikin garin Gombe, ya shiga wuraren harkar ilimi da yawa inda ya yi karance-karance iri daban-daban.

Ya yi karatu a cikin garin Gombe a wurin Malam Sa'idu da Malam Adamu da wasu manya-manyan malamai da ya yi karatu a wajensu irin na zaure.

A zaurukan da ya yi karatu a Gombe, ya sake tisa karatun Ƙawa'idi da Ahalari da Ishmawi da Iziya da Risalah da sauran litattafai.

Ya ce "malamin da na sauke tafsiri a wurinsa sau uku, ya kan naɗa ni ya ajiye ni ya ce idan ɗalibai sun zo na koya musu tafsirin Al-Ƙur'ani, shi ma na samu shekara sun kai biyar zuwa shida a ƙarƙashinsa", in ji shi.

Abin farin ciki da malam ba zai manta da shi ba

Sheikh Adamu ya bayyana cewa babban abin farin cikin da ba zai manta da shi ba shi ne samun Al-Ƙur'ani da ya yi.

Ya ce ba zai taɓa mantawa da wannan ba saboda babbar kyauta ce daga wajen Allah (S.W.A)

Abin da ya fi faranta wa malam rai

Sheikh Adamu ya ce abin da ya fi faranta masa rai shi ne ya ga yaro yana ƙoƙarin abubuwa guda uku a cikin rayuwa, wato yana neman ilimi da riƙon addini da kuma ƙoƙarin sana'a.

Malam ya ce babu abin da ya fi ba shi takaici irin kamar ganin matashi ya lalata rayuwarsa, wato ba ilimi ba addini kuma babu sana'a.

Surar da Malam ya fi so a cikin Al-Ƙur'ani

"Shi Al-Ƙur'ani ko ina idan ana karanta shi ana samun shauƙi, amma idan wani ne yake karatu, nake saurare, wato babu kamar Suratul Safat. Wato ayoyinta gajeru ne amma ina son ji daga wani yana karanta su," in ji Malam.

Malam ya ce surar na saka shi nishaɗi amma duk da haka ita ma Suratul Waƙi'a yana jin daɗinta domin wasu lokutan yakan karanta surar a cikin sallolinsa

Tambayoyin da aka fi yi wa Malam

Sheikh Adamu ya bayyana cewa tambayoyin da aka fi yi masa, tambayoyi ne da suka shafi zamantakewar aure ko mutuwar aure ko kuma yadda za a yi a gyara shi.

"Ni kaina na fi sha'awar na yi magana kan abin da zai gyara auratayyar mutane, idan na samu wannan gaɓar a cikin karatu ban cika barinta haka kawai ba saboda ina ganin idan al'umma aurenta ya yi kyau kuma ya zama cewa gidaje sun yi kyau toh al'umma ta samu dukkan abin da ya kamata kuma dukkan rayuwa za ta tafi ta zamo daidai," in ji shi.

Abincin da malam ya fi so

Malam ya ce bai cika cin abincin gargajiya ba irin su tuwo da sauransu inda ya ce yakan ɓata masa ciki ma.

Malam ya ce abin da zai iya ci ko da ba daɗinsa zai ji ba kuma ba zai yi masa illa ba shi ne soyayyen dankalin Turawa da na Hausa.

Ya ce duk wani abinci irin su shinkafa da tuwo har nama duk ba cinsu yake yi ba inda ya ce tun asali ma idan ya ci nama amai yake yi.

Batun iyali

Malam ya ce a halin yanzu matarsa guda ɗaya, kuma matarsa ta farko ta rasu sai ya auri wata. Malam ya ce yaransa sun kai guda goma, maza shida mata huɗu.