Ku San Malamanku tare da Sheikh Abu Ammar
Wani malamain addinin Musulunci a jihar Katsinan Najeriya Sheikh Muhammad bn Usman Abu Ammar, ya ce zafafan huɗubobin da yake yawan yi a kan danne haƙƙin talakawa da hukumomi ke yi ne ya sa ake yawan tsare shi.
Malamin ya faɗi hakan ne a shirin Ku San Malamanku na BBC Hausa.
Sheikh Abu Ammar wanda aka taɓa tsare shi a hannun jami'an tsaro har sau biyu, ya ce hakan bai taɓa girgiza shi ko sanyawa ya ja da baya a "ƙoƙarinsa na tsage gaskiya ba."
Malam ya ce huɗubobi masu zafi da yake yi kan yadda ake zaluntar al'umma ne ya sa ake yawan kama shi.
"Babu abin da ke ɓata min rai irin na ga ana zaluntar ɗan adam.
"Shi ya sa nake huɗuba mai zafi a kan danne haƙƙin dan adam musamman ta ɓangaren shugabanni.," a cewarsa.
"Na kan yi huɗuba mai zafi kan halin ko in kula da hukumomi ke yi da halin da al'umma ke ciki. Raina kan baci idan na ga al'umma na cikin yanayi,' kamar yadda ya bayyana.
Sheikh Abu Ammar ya ce an sha kiransa wajen jami'an tsaro har bai san iyaka ba, a gayyace shi na yi magana a kan hudubar da yake yi.
"Amma sau biyu dai aka taɓa tsare ni ta fuskar abin da ya shafi kira ga gwamnati ta kula da haƙƙin talaka.
"Hukumomin kan ji zafi idan suka ji wani malami yana tunatar da su," in ji shi.
Sai dai malam ya ce kamun ba ya ba shi tsoro ko razani shi, musamman idan ya ga tarihin magabata kan yadda wasun su ma suka mutu a tsare.
"Na kan ji karashi ma idan aka tsare nin don hakan na nuna irin hidimar da na yi wa addini," ya ƙara da cewa.
Wane ne Sheikh Abu Ammar?
An haife shi a garin Funtua na jihar Katsina ranar 5 ga watan Oktoban shekarar 1978.
Ya fara daga karatun allo a wajen ƙanin mahaifiyarsa. Ya yi makarantar Firamare ta Kadawa a Dandume.
Malam ya ci gaba da karatun boko da na addini a Samaru a Zariya.
Ya yi saukar Al-Kur'ani da hadda a makarantar Madarasatu Islamiyatul Fauziyya. Ya sha wakiltar makarantar a musabaƙar Al-ƙur'ani.
Ya yi karatun littattafan addinin Musulunci sosai a Zariya.
Daga baya ya shiga makarantar ATC a Katsina, sannan ya halarci Jami'ar Musulunci a Katsina, inda ya kammala a 2009.
A 2010 ya samu gurbin ƙaro karatun digiri na biyu a Sudan inda ya kammala a shekarar 2012.
Ya samu aikin koyarwa a fannin harshen Larabci a shekarar 2013 a Kwalejin Ilimi ta Tarraya a Katsina.
A shekarar 2018 kuma ya koma koyarwa a Jami'ar Tarayya ta Dutsinma inda har yanzu yake can.
Ya samu gurbin ƙaro karatu a Jami'ar Iskandariyya a Masar, har yanzu yana yi bai kammala ba.
Malam na da mata biyu da ƴaƴa bakwai, shida maza ɗaya mace.
Da'awah
Kokarin wayar da kan al'umma kan ci gaban rayuwa shi ne babban abin da ya fi mayar da hankali a kai a da'awarsa.
Sai kuma jan hankali shugabannin kan wanzar da adalci, kamar yadda ya ce..
Kan tambayar da aka fi yi masa kuwa, ya ce an fi masa tambayoyi a kan aure, ko a majalisi ko ta hanyar aika masa da saƙo.
Sai kuma ana masa tambayoyi a kan kasuwancin zamani.
Malam ya ce ba zai taɓa mantawa da zuwansa aikin Hajji ba a rayuwarsa, "musamman lokacin da na yi ido huɗu da Dakin Ka'aba.
"Na yi ta hawaye ba ƙaƙƙƙautawa."
Abincin da Malam ya fi so shi ne kwaɗon zogala. Sannan yana son yin wasan ƙwallon tenis sosai.











