Muhammadu Buhari: Shugaban Najeriya ya fasa zuwa Zamfara saboda hazo

Shugaba Muhammadu Buhari ya soke ziyararsa zuwa jihar Zamfara a ranar Alhamis sakamakon rashin kyawun yanayi da ya jawo hazo.
Daya daga cikin masu taimaka masa a shafukan sada zumunta Buhari Sallau ne ya wallafa hakan a shafinsa na Facebook.
Tun da fari an tsara cewa shugaban zai bi helikwafta ne daga Sokoto inda ya fara ziyarta zuwa Gusau.
Sanarwar ta ambato gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya ce: "Shugaban ƙsa ya yi magana da ni ya kuma umarce ni da na bai wa al'ummar jihar Zamfara haƙurikan wannan sauyi da aka samu.
"Shugaban ƙsa ya ce ya sauya ranar ziyarar tasa zuwa mako mai zuwa kuma za a sanar mana da sabuwar ranar ziyarar nan gaba kaɗan.
Gwamna Matawalle ya kuma ce: "Wasu manyan shugabannin tsaro a yanzu haka suna Katsina amma ba za su iya zuwa Zamfara ba saboda rashin kyawun yanayi
"Muna miƙa godiyarmu ga shugaban ƙsa saboda ƙaunar da yake nuna wa jiharmu," in ji Matawalle.
A yau ne Shugaba Buhari ya fara sauka a Sokoto inda ya ƙaddamar da sabon kamfanin siminti na BUA.
An hana zirga-zirga a yayin ziyarar Buhari a Gusau
Gabanin ziyarar tasa da aka sa rai zai kai a ranar Alhamis, an tsara Shugaba Muhammadu Buhari zai sauka a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, a wata ziyarar wuni guda da zai kai.
Tun a jajiberin ziyarar gwamnatin Zamfara ta bayar da sanarwar dakatar da zirga-zirgar ababen hawa ta tsawon sa'a uku a yayin ziyarar ta shugaban ƙasa.
Gwamnatin jihar dai ta ce shugaban na Najeriya zai je Zamfara ne domin jajanta wa al'ummar jihar game da miyagun hare-haren 'yan fashin daji na baya-bayan nan musamman a ƙananan hukumomin Anka da Bukkuyum.
Kwamishinan Yaɗa labarai na jihar Zamfara, Malam Ibrahim Magaji Dosara, ya shaida wa BBC cewa tuni suka kammala shirye-shiryen tarbar shugaban kasar.
Ya ce baya ga ta'aziyya da jajen da Shugaba Buhari zai yi wa al'ummar ta Zamfara, zai kuma kara wa sojoji Najeriya da ke jihar kwarin gwiwa a kan irin samame da sauran ayyukan da suke yi wajen fatattakar 'yan bindigar da ke kai hare-hare a jihar da ma sauran jihohi.
Kwamishinan Yaɗa labaran ya ce daya daga cikin manufar ziyarar shugaban kasar a Zamfara ita ce domin ya sanyaya zukatan al'ummar ta Zamfara tare da nuna musu cewa yana tare da su.
Malam Ibrahim Dosara ya ce," Ba jajen Anka da Bukkuyum kadai Shugaba Buhari zai yi ba, zai yi jaje ne ga dukkan iyalan wadanda suka rasa wani nasu a hare-haren 'yan bindigar a jihar Zamfara".
A cewarsa a yayin ziyarar shugaban kasar zai gana da jami'an tsaron da ke aiki a jihar da malamai da sarakunan gargajiya da kuma iyalan wadanda suka rasa ransu a yayin hare-haren.
Tuni dai gwamnatin jihar ta bukaci al'ummarta da su kiyaye da dukkan wasu dokoki a yayin ziyarar shugaban kasar.
Karin bayani
Al'ummar jihar da ma wasu a sauran jihohi sun jima suna tsokaci a kan rashin zuwan shugaban Najeriya Zamfara don jajantawa al'ummar jihar a kan irin masifar da suke gani ta hare-haren 'yan fashin daji.
Jihar Zamfara dai na daya daga cikin jihohin Najeriya musamman a yammacin kasar da ke fama da hare-haren 'yan fashin daji da satar mutane abin da ala tilas mazauna yankuna da dama na jihar suka bar muhallansu don tsira da ransu.
Kusan kananan hukumomin jihar na fuskantar wadannan hare-hare, inda hatta noma ma a wasu yankunan aka daina saboda yadda fashin dajin ke kai wa manoma hari su kashe su a cikin gonakinsu.
To ko wanne tasiri ziyarar shugaba Buharin zata yi wajen tabbatar da tsaro a jihar ta Zamfara? wannan shi ne abin da al'ummar yankin ke jira su gani.











