Abu shida da suka kamata ku sani kan alaƙar Buhari da Kaduna

.

Asalin hoton, BUHARI FAMILY

An wallafa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, wanda yanzu haka yake ziyarar aiki ta kwana biyu a Kaduna, ɗan asalinsa jihar Katsina ne kuma ya fito ne daga garin Daura, sai dai yana da kyakkyawar alaƙa da Jihar ta Kaduna.

Shugaban dai ya yi makarantar firamare a garin Daura da Mai'adua sa'annan ya yi makarantar Middle ta Katsina a karatunsa na sakandire.

Bayan ya kammala sakandire ne ya soma ƙulla alaƙa da garin Kaduna. BBC ta yi nazari kan alaƙar Shugaba Buhari da Jihar Kaduna da kuma yadda Kaduna ta shafi rayuwarsa da ta iyalansa.

Akasarin rayuwarsa ya yi ta ne a Jihar Kaduna

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shafe akasarin rayuwarsa a Jihar Kaduna, domin tun kafin ya zama shugaban ƙasa a karo na biyu, gidansa da yake zama da iyalansa yana a Kaduna, kuma idan ya je Kaduna a can yake sauka.

Za a iya cewa Shugaba Buhari ya soma alaƙa da Kaduna ne tun a 1962 a lokacin da ya shiga Kwalejin horas da ƙananan hafsoshin sojoji ta Nigerian Military Training College wadda daga baya aka mayar da ita Nigerian Defence Academy wato NDA.

Buhari yakan je Daura hutu da sauran wurare hutawa ko kuma ayyuka amma dai gidansa na zama da iyalansa duk suna Kaduna.

.

Asalin hoton, Getty Images

A Kaduna ya haɗu da matarsa ta farko da ya aura

Shugaba Buhari ya haɗu da matarsa ta farko Safinatu a Kaduna inda suka yi aure a 1971.

Ko bayan da aka yi wa Buhari juyin mulki a 1985, shi da iyalansa sun koma Kaduna da zama bayan an sako shi daga ɗaurin da aka yi masa a wani kurkuku da ke Benin.

Ko bayan da ya rabu da matarsa ta farko ya auri Aisha, sun ci gaba da zama a Kaduna har lokacin da ya zama shugaban ƙasa a karo na biyu.

Ƴaƴan Buhari sun yi makaranta a Kaduna

.

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

A wani littafi da wani Bature mai suna John N. Paden ya rubuta game da Muhammadu Buhari, ya lissafo ƴaƴan Shugaban da makarantun da suka yi kuma sun yi karatu a Kaduna.

A littafin, Fatima ta yi karatu a Government College Kaduna da Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, sai kuma Nana Hadiza ta yi makarantar sakandire a Essence da ke Kaduna haka kuma Safinatu ma ta yi makaranta a Essence Kaduna.

Sai Halima da Yusuf da Zahra da Aisha da Noor dukansu sun yi makaranta a Kaduna International School.

Akasarin manyan abokan Buhari a Kaduna suke

Ganin irin alaƙar da Buhari yake da ita da Jihar Kaduna, akasarin abokan shugaban a Kaduna suke. Haka kuma tsofaffin abokan aikin soja waɗanda suka yi aiki tare suna da gidaje a Kaduna.

Alal misali, Marigayi Janar Shehu Musa Yar'adua da kuma Kanal Ahmadu Ali mai ritaya su ne makwabtan Shugaba Buhari a Kaduna.

Akwai tsohon gwamnan Kaduna AVM Usman Mu'azu shi ma yana shiri da Buhari kuma gidansa a Kaduna yake.

Haka kuma manyan abokansa irin su Marigayi Sarkin Borgu Halliru Ɗantoro da Marigayi Abba Kyari duka suna da gidaje a Kaduna kuma sun yi rayuwa da Buhari a Kaduna.

An taɓa kai wa Buhari hari a Kaduna

.

Asalin hoton, Premium Times

A shekarar 2014, wani abin tashin hankali ya faru da Shugaba Buhari inda aka kai wa ayarin motocinsa hari ta hanyar tayar da bam.

Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa wani ne a cikin mota ƙirar Sienna ya dumfari motar da Buhari ke ciki inda ya tayar da bam ɗin.

Duk da Buhari bai ji rauni ba, amma masu tsaron lafiyarsa har mutum uku sun ji rauni. Bayan harin da aka kai masa a Unguwar Kawo, a ranar gwamnan jihar na lokacin Mukhtar Ramalan Yero ya saka dokar hana fita.

Daga Aso Rock sai Kaduna

Da alama Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari idan ya sauka daga mulki a 2023 Kaduna zai koma da zama.

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El Rufai ne ya tabbatar da hakan inda ya ce shugaban zai ci gaba da zama a Kaduna a ƙarshen wa'adin mulkinsa.