India ta dakatar da kungiyar agaji mai bambancin addini

Kungiyar mishan ta Missionaries of Charity tana gudanar da ayyukan jin-kai na bayar da abinci da makarantu da asibiti a fadin India

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kungiyar mishan ta Missionaries of Charity tana gudanar da ayyukan jin-kai na bayar da abinci da gudanar makarantu da asibitoci a fadin India
An wallafa

Gwamnatin India ta ki sabunta takardar izinin samun tallafin kudi daga kasashen waje na kungiyar ayyukan jin-kai wadda matar nan 'yar mishan Mother Teresa ta kafa.

Kungiyar, The Missionaries of Charity tana da dubban mata masu hidima a coci da ke sa ido a ayyukan jin-kai da suka hada da gidajen marayu ko yaran da aka yi watsi da su da makarantu da asibitoci da kuma gidajen kula da masu fama da cutar daji da ke da sauran 'yan kwanaki su rayu.

A ranar Kirsimeti ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta India ta fitar da wata sanarwa, wadda a cikinta ta ce ba ta sabunta lasisin ayyukan kungiyar ba saboda wasu dalilai da ta ce masu illa.

Matsu tsatstsauran ra'ayin addinin Hindu sun dade suna zargin kungiyar ta 'yan mishan da amfani da ayyukanta na jin-kai wajen mayar da mutane Kiristoci. Amma kungiyar ta musanta dukkanin zargin.

'Yar mishan Mother Terersa kenan tare da wasu yara da take kula da su a Kolkata, India a watan Disamba na 1980

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yar mishan Mother Terersa kenan tare da wasu yara da take kula da su a Kolkata, India a watan Disamba na 1980

Kungiyar agajin ta tabbatar da wannan mataki da gwamnatin Indiyar ta dauka a kanta ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, inda ta ce daga yanzu ba za ta sake amfani da wani asusun banki na samun kudin tafiyar da ayyukanta ba har sai an sasanta a kan batun.

Ita dai ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta India wadda ta yi hukuncin, ba ta yi bayani dalla-dalla ba a kan abin da ya sa ta yi hakan.

Kungiyoyin masu tsatstsauran ra'ayin addinin Hindu a baya suna zargin kungiyar 'yan mishan din da janye mutane zuwa addinin Kirista, ta hanyar bayar da taimakon abinci da ilimi kyauta da samar da matsuguni ga talakawa 'yan Hindu da sauran talakawa.

Hukumomin na India sun dauki wannan mataki ne yayin da ake ci gaba da kai hare-hare da muzguna wa mabiya wasu addinai 'yan tsiraru a kasar a watannin nan.

Tarwatsa bukukuwan Kirsimeti da wasu 'yan kungiyoyin sa-kai na 'yan Hindu suka yi a cikin kwanakin nan a sassan kasar ta India ya janyo surutai da tayar da jijiyar wuya.

Tun da farko babban ministan Bengal ta Yamma, Mamata Banerjee, ya sha suka bayan da ya sanya wani sakon tuwita, na sanar da matakin gwamnati na dakatar da asusun kungiyar ta mishan ta Mother Teresa.

To amma kuma nan da nan gwamnatin ta kums fito ta musanta cewa an dakatar da asusun.

Ita dai kungiyar wadda take da cibiya a Kolkata ( Calcutta ) a gabashin India, marigayiya 'yar mishan ta Katolika ce Mother Teresa wadda ta koma India da zama daga kasarta Macedonia ta kafa ta a shekarar 1950.

Tana daya daga cikin fitattun kungiyoyin ayyukan jin-kai na Katolika.

Mother Teresa ta samu lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel a shekarar 1979 a kan ayyukan da take yi na jin-kai.

Kuma Paparoma Francis ya ayyana ta a matsayin waliyya a 2016, shekara 19 bayan rasuwarta.