Tsohuwa mai shekara 104 da ta koma makaranta

Bayanan bidiyo, Tsohuwa mai shekara 104 da ta koma makaranta
An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Kuttiyamma ta kwashe tsawon rayuwarta tana kula da wasu.

Ba ta taba zuwa makaranta ba kuma an aurar da ta ita tana da shekara 16.

Yanzu shekarunta 104, kuma ita ce ta samu maki mafi yawa a ajinsu da ke makarantar yaki da jahilci a India.

Jikokin Kuttiyamma ne suka karfafa mata gwiwar neman ilimin karatu da rubut.