Ku San Malamanku tare da Sheikh Khalifa Abba Al-Amin Banki
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
An haifi Sheikh Khalifa Abba Al-Amin Banki a ranar 1 ga watan Zhul Hajj shekarar 1398, wanda ya yi daidai da ranar 22 ga watan Nuwambar shekarar 1967 a garin Banki.
Sheikh Khalifa ya taso ne a garin Banki da ke Ƙaramar Hukumar Bama ta jihar Borno kuma duk karatun da ya yi, ya yi shi ne a gaban mahaifinsa da kuma a wurin yayansa wato Sheikh Sherrif Ibrahim Saleh.
Ya bayyana cewa kusan duk wani karatunsa da ya yi na addini da na Larabci ya yi shi ne a gidansu.
Ya ce tun bai kai shekara 20 ba ya samu ya kammala haddar Al-Kur'ani mai girma.
Malamin ya ce a ɓangaren karatun boko kuwa, ya soma ne tun daga firamare ya je zuwa sakandire da gaba da sakandare inda a halin yanzu ma yana ci gaba da karatun da burin zama dakta.
A fannin wasanni irin na ƙuriciya kuwa, malamamin ya ce ba su samu lokacin yin wasanni ba ganin cewa gidansu na ilimi ne mafi yawan lokuta ana karatu ne da sha'anin addini.
Sheikh Khalifa ya ce surar da ta fi ba shi wuya wajen hadda ita ce Suratul Rahman haka kuma ya fi son Suratul Ikhlas.
Malamin ya bayyana cewa abin da ba zai taɓa mantawa da shi ba na farin ciki shi ne ranar da mahaifinsa ya ce masa duk darusan da yake yi shi ne zai ci gaba da yi.
Ya ce ko bayan da mahaifinsa ya rasu, sai Sheikh Ibrahim Saleh ya fito ya ƙara faɗa masa cewa duk wasu abubuwan da mahaifinsa ke yi da suka shafi karantarwa shi ne zai ci gaba a halin yanzu.
Ya kuma ce babban baƙin cikin da ba zai manta da shi ba shi ne fitinar Boko Haram da ta addabi musamman yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Sheikh Khalifa ya bayyana cewa wannan matsalar ta sa an samu koma baya musamman a ɓangaren addini bayan haka kuma ya shafi ɓangaren kasuwancin inda malamin ya ce bayan wannan lamari babu abin da ya tsana kamar haka.
Ya kuma bayyana cewa babban abin da yake faranta masa rai shi ne ya ga al'umma sun yi zaman lafiya ba tare da nuna bambancin addini ko aƙida ko ƙabila ba.
Sheikh Khalifa kuwa ya ce a ɓangaren abinci kuwa ya fi son kunun alkama wanda ya ji gyaɗa.
A ɓangaren iyali kuwa malamin ya ce yana da mata uku da kuma yara 11 haka kuma malamin ya ce babban burinsa shi ne ya dage kan koyarwar addini har ƙarshen rayuwarsa.
Haka kuma malamin ya ce yana kuma so ya bar litattafai da ko ba ya raye al'ummar Musulmai za su iya amfana da litattafan.











