Firaministan Burtaniya zai jaddada wa duniya hadarin dumamar yanayi

Boris Johnson

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Firaministan Burtaniya Boris Johnson, zai bukaci gwamnatocin kasashen duniya a kan su rufe sauran gibin da ya rage a tsakaninsu a taron sauyin yanayi na duniya da ake yi a birnin Glasgow, a Larabar nan.

Masu shiga Tsakani domin samun daidaito daga kusan kasashe dari biyu ne ke kokarin samun matsaya a kan lokacin da ya kamata a daidaita a kansa na rage hayaki mai haifar da dumama ko sauyin yanayi.

Masu hangen jirgi a samaniya

Asalin hoton, OTHERS

Bayanan hoto, Masu hangen jirgi sun ce taron sauyin yanayin ya ba su damar da kusan sau daya ake iya samu a rayuwa su hango jirgin saman da ba kasafai ake gani a Scotland ba

Firaministan zai sake komawa Glasgow, domin matsa wa ministoci da sauran manyan wakilai na gwamnatoci da hukumomi, domin ganin sun kara matsawa gaba sosai a alkawura da tabbacin cimma muradun da ake son ganin an kai ga samu na rage yawan hayaki mai dumama yanayi.

Mista Johnson zai gaya musu keke da keke cewa, wajibi ne su kawar da duk wani wakafi ko aya da ke zama tarnaki ga wannan buri, ta yadda hanya za ta kasance dodar wajen ganin an rage yawan dumin da kasashe ke sanya wa duniya zuwa lamba daya da rabi a ma'aunin selshiyas (Celsius).

An ruwaito Firaministan yana cewa har yanzu akwai dimbin aiki a gaba, yana cewa a yau din zai gana da ministoci da masu shiga Tsakani domin ji daga garesu, inda aka ci gaba da kuma inda za a dinke wata baraka.

Yana cewa "Wannan abu ne da ya fi wata kasa daya tilo girma, kuma lokaci ne da kasashe za su kawar da duk wani bambancin da ke tsakaninsu su hada kai domin amfanin wannan duniya da kuma al'ummarmu.''

Kira a taron sauyin yanayi

Asalin hoton, Getty Images

Wadanda suka shirya taron kolin na duniya kan sauyin yanayin za su yi kokarin ganin an cimma matsaya kan tsari na bai daya da za a rika bayar da rahoto kan sauyin yanayi

Ko da yake wannan wani batu ne na kwararru, to amma zai taimaka wajen tabbatar da ganin alkawuran da aka yi a taron ana aiwatar da su ta yadda za a iya gani ko auna irin cigaban da ake samu ko akasinsa.

Matakin da kasashe za su kai wajen cika alkawuran da suka yi shi ne zai nuna makomar wannan duniya tamu.

Ana sa ran wakilai za su tuntubi shugabanni da majalisun dokokin kasashensu, bayan an wallafa daftarin matakai da shawarwarin da aka cimma a safiyar Larabar, inda su kuma za su tattauna a kan matsayarsu a kan daftarin.

Wannan zai kasance mai muhimmanci, musamman ga kasashen da shugabanninsu ba su halarci taron ba a farkonsa.

Kasashen da suka hada da wasu daga cikin manya-manyan masu gurbata duniyar kamar su China da Rasha da Brazil.