COP26: Kalubale huɗu da ke gaban mahalarta taro kan sauyin yanayi

cop26

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sauyin yanayi
    • Marubuci, Daga Matt McGrath
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan muhalli
  • An wallafa

Shugabannin kasashen duniya sun isa Glasow domin halartar taron ƙoli kan sauyin yanayi wato COP26, inda za a buƙace su da su rage iskar da ke guraɓata muhalli da ke haifar da ɗumamar yanayi domin rage tsananin zafi a duniya.

Yayin da masu tattaunawa ke shirin shafe tsawon makonni biyu suna tattaunawa, ga manyan ƙalubale biyar da ya kamata a shawo kansu.

1. Aminci

Matsalar zafi mai tsanani da kwal maras inganci ba su ne kalubale ba. Babban kalubalen da masu tattaunawa suke fusktanta a wannan taro shi ne aminci ko rashinsa.

An samu koma baya a matsayar da aka cimma a taron ƙolin sauyin yanayi da aka yi a shekarar 2015 a birnin Paris.

A wancan lokacin Amurka da China sun cimma matsaya. Bayan shekara hudu da mulkin Donald Trump da kuma gaba da suka yi wa juna, a yanzu kasashen biyu sun saka wa juna ido.

More on Climate Change bottom strapline

COP26 Taron kolin sauyin yanayi - Muhimman batutuwa

  • Sauyin yanayi na daya daga cikin manyan matsalolin duniya. Dole ne gwamnatoci su yi alkawarin rage yawan gurbataciyyar iskar da ake fitarwa domin rage dumumar yanayi.
  • Taron kolin da ke gudana a Glasgow shi ne inda sauyi zai iya faruwa. Ya kamata ku lura da alkawuran da manyan kasashen duniya masu gurbata muhalli suka yi, irinsu Amurka da China da kuma ko kasashe mataulata na samun taimakon da suke bukata.
  • Rayuwarmu za ta canza. Matakin da za a dauka a wannan wuri na iya tasiri ga ayyukanmu, da yadda mu ke cin abinci da kuma tafiye-tafiye.
More on Climate Change bottom strapline

Matsin lambar da hadin gwiwar tsibirai da kasashe masu tasowa da kuma Tarayyar Turai suka yi domin ciyar da abubuwa gaba a Faransa a shekarar 2015 a yanzu ba shi da ƙarfi.

Akwai kuma matsalar kudi: Kasashen duniya sun kasa cika alkawuran da suka yi na samar da dala biliyan 100 domin taimaka wa kasashe masu fama da bakin talauci a kan sauyin yanayi.

Duk yadda aka duba, abu ne da ya yi wa aminci illa.

Da yake jawabi a taron G 20 da aka yi birnin Rome gabanin tashinsa zuwa Glasgow domin halartar na sauyin yanayi, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guteres ya jaddada muhimancin batun aminci.

"Idan muna son samun nasara ta gaske, muna bukatar daukar karin matakai," in ji shi.

"A yanzu aminci ya yi ƙaranci, akwai manyan tambayoyi a kan sahihanci."

Idan ba a shawo kan wannan matsalar ba to zai yi wuya Taron Glasgow ya yi tasiri.

2. Sahihanci

Mabudin kowace nasara a Glasgow dole ne ya zama amincin kasar da ta karbi baƙuncin taron.

Ana ganin Faransa ta kafa shinge a kan yadda shugabanci na gari lokacin da ta karbi bakuncin taron a shekarar 2015.

Alok Sharma

Asalin hoton, IISD/ENB - Kiara Worth

Bayanan hoto, Ministan Birtaniya Alok Sharma a taron sauyin yanayi COP26

Birtaniya na fuskantar kalubale a wannan fannin, ko da yake tana da kudi a banki.

"Birtaniya ta kasance jagora a shekaru da dama da suka gabata," in ji Kaveh Guilanpour, wanda ya dade yana shiga tsakani kuma a yanzu jami'i ne a wata cibiyar kula da muhalli.

Alkawarin da gwmnatin kasar ta yi a taron Paris na ganin ta matukar rage fitar da iskar da ke gurbata muhalli nan da shekarar 2050 ya nuna cewa da gaske take.

Sai dai a gefe guda, gwamnatin Birtaniya ta fuskanci matsala game da shirinta da ya shafi wata mahakar kwal a Cumbria a makon da ya gabata.

3. Aikin da ke gaba

Daya daga cikin manyan kalubalen da ake fuskanta a wannan taron ƙoli shi ne jan aikin da ke gaba.

A bara an ɗage taron sauyin yanayi saboda annobar korona amma kuma ba a samu nasara ba a kokarin da aka riƙa yi wajen ganin an yi taron ta intanet.

Wakilan kasashen sun ce a shirye suke su yi magana amma sun ce ba za su dauki mataki ba idan ba ganawar ido da ido ba ce.

A don haka taron Glasgow na da babban buri a gabansa musamman a kan batun da ya shafi yadda kasashe za su samar da kudi a kan sauyin yanayi.

Wakilai

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu mahalata taron sauyin yanayi da aka yi a Copenhagen a 2009 na barci

Akwai kuma bayanai masu sarƙaƙiya game da yadda ya kamata a aiwatar da yarjejeniyar Paris da har yanzu ba a warware ba.

Tambayoyin sun hada da gaskiya da samun lokaci guda a kan yadda za a rage hayakin da ke gurbata muhalli.

4. Yadda tsarin yake

Akwai masu ganin cewa shawarwarin Majalisar Dinkin Duniya ba su dace da manufar ba.

Akwai bukatar ganin cewa kasashe 197 sun cimma matsaya amma idan aka dubi yadda aka tsara tattaunawar a hukumance a zahiri abu ne mai wuya a yi tattaunawar da za ta yi tasiri.

A wannan taron Birtaniya ta ƙuduri aniyar ganin cewa ta nuna wa duniya cewa yaƙi da sauyin yanayi abu ne mai kyau ga duniya da harkokin kasuwanci.

Tana son ta shawo kan batutuwa da suka shafi sare itatuwa, kwal da kare muhalli.