Bukatun da Shugaba Buhari ya gabatar a taron zuba jari na Saudiyya

Shugaba Buhari

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Taron saka jari da ake gudanarwa a Saudiyya dama ce ta gabatar da buƙatu da cin gajiyar taron.

Taron na kwana uku wanda aka soma a ranar Talata shi ne karo na biyar da Sarkin Saudiyya ke jagoranta a Riyadh babban birnin ƙasar.

Taron ya ƙunshi shugabannin ƙasashe da manyan ƴan kasuwa masu saka jari da bankuna, kuma an bayyana cewa ya ƙunshi kamfanoni sama da 5,000 da ke halartar taron.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana cikin shugabannin duniya da suka halarci taron wanda aka yi wa take da 'zuba jari kan inganta rayuwar al'umma'.

A cikin jawabin da ya gabatar a wurin taron, shugaba Buhari ya ce Najeriya ta mayar da hankali kan wasu manufofi na ci gaba, ta hanyar rage dogaro da arzikin fetir zuwa noma da fasahar sadarwa da kuma ma'adinai.

Ƙasar kuma a cewar Buhari ta mayar da hankali kan yaƙi da rashawa da matsalar tsaro da sauyin yanayi da ƙaddamar da shirin tallafawa al'umma.

Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu a hirarsa da BBC game da taron ya ce "taro ne da za a iya kiransa kamar tsarin bajekoli" tare da bayyana wasu guzurin buƙatu da Najeriya ta gabatar a taron.

Da me Najeriya ta je?

A cikin jawabinsa, Buhari ya ce saka jari kan ilimi da fannin kiwon lafiya da karfafa wa matasa da kawar da talauci da sauyin yanayi da samar da abinci, zai taimaka sosai wajen sake farfado da tattalin arzikin duniya bayan annobar korona.

Kuma Malam Garba Shehu ya ce Buhari ya tallata wasu buƙatun Najeriya kamar man fetur wanda shi ne ƙashin bayan arzikin duniya.

Ya ce wata biyu da suka wuce Buhari ya sa hannu a kan sabuwar dokar man fetur wacce ta ba da izinin saka jari daga kasar waje - "ka saka jari ka kuma fita da shi cikin sauki yadda kaka so."

Ya ce an sauye-sauye wajen haƙar ma'adinai inda aka sassuta doka don ba ƴan ƙasashe waje damar shiga su zuba jari.

"Yawan al'umma miliyan 200 baiwa ce da Allah Ya yi wa Najeriya, ita ma haja ce. Kuma a cikin ƴan Najeriyar akwai kwararru masu ilimi da za a yi sha'awar a zo don za a samu ma'aikata. Kamar aikin gona, irin dazuzuzuka da za a iya mayar da su zuwa gonaki. A bunkasa asibitoci da makarantu da tituna,"

"Ka gina titi ka dinga karbar haraji don ka mai da kudinka."

"Buhari duk ya tallata su kuma abin ya samu kyakkaywar karbuwa," in ji shi.

Ribar da Najeriya ke sa ran samu

Gwamnatin Najeriya ta ce taron fage ne na janyo hankalin duniya ga abin da kuka mallaka da kuma kasuwar da kuke da ta ita

Za a nuna wa duniya da masu kuɗi da masu saka jari su fahimci cewa lallai idan ka shigo Najeriya da abu za ka samu riba mai yawa saboda irin dumbin al'umma da arziki da kasar ke da shi, a cewar Garba Shehu.

Ya ƙara da cewa za a nuna wa masu saka jari kan abubuwan da ke bukatar a shigo da jarin a kafa kamfanoni don a ci moriyarsau a amfana daga kowanne ɓangare.

Sai dai Najeriya na cikin ƙasashe da ke fama da matsalar tsaro inda ƴan Boko Haram suka shafe shekaru sama da 10 a shiyar arewa maso gabashi da kuma ƴan bindiga masu fashin daji da satar mutane a arewa maso yammacin Najeriya da matsalar ƴan a ware a kudancin Najeriya.

Matsalar tsaro na iya zame wa yan kasashen waje barzanar zuwa zuba jari a Najeriya - kuma shi kansa Buhari ya ce matsalar tsaro barazana ce ga zuba jari a Najeriya.