Abubuwa biyar masu ban mamaki waɗanda ke tasiri kan sauyin yanayi

Abubuwan sun ba wannan mata mamaki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Abubuwa iri-iri masu ban mamaki da ke fitar da hayaki mai gurbata muhalli
An wallafa

Dukkanmu mun san nau'ukan abubuwan da za su iya rage tasirinmu kan dumamar yanayi.

Rage yawan tafiye-tafiye da jirgin sama. Sannan kuma yana da kyau mu rika amfani da motocin lantarki tare da yawaita cin abincin da aka shuka ba wanda aka sarrafa ba.

Amma akwai wasu abubuwa da watakila ba ku san da su ba.

Ga abubuwa biyar da ba a saba gani ba waɗanda ke taimakawa wajen janyo sauyin yanayi.

1. Shinkafa

Shinkafa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shinkafa ita ce abincin da mutane biliyan uku da rabi suke ci a duniya

Fiye da rabin al'ummar duniya na cin shinkafa a matsayin abincinsu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Amma shuka ce mai matsala wajen nomawa.

Ana bukatar ruwa mai yawa sosai a gonakin shinkafar kuma wannan na haifar da kananan kwayoyin cuta a cikin kasa da ke samar da iskar Methan wadda ta fi hayakin carbon dioxide illa wajen gurbata muhalli.

Kashi daya zuwa biyu cikin dari na iskar da ke gurbata muhalli daga noman shinkafa ake samunta kuma filayen noma da ake konawa bayan an girbe ta suna taimakawa wajen fitar da hayaki mai gurbata muhalli a sararin samaniya.

Masu bincike na aiki a sassan duniya don samar da nau'ukan shinkafa wadanda ke samar da albarkatu masu yawa kuma ba sa bukatar fadama mai ruwa sosai domin su tsiro domin rage tasirin noman shinkafa a kan dumamar yanayi.

2. Amfani da Intanet

Wata mata na aiki da komfutarta a cikin daki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kusan kashi 60 cikin dari na al'ummar duniya na amfani da intanet

Binciken intanet mai sauki yana haifar da giram kalilan na hayaki mai gurbata muhali, saboda makamashin da ake bukata domin tafiyar da na'urorinku da kuma kunna hanyar sadarwarku.

Ya yi kama da abin da bai taka kara ya karya ba amma alkaluman baya-bayan nan sun nuna cewa mutum biliyan 4.66 ke amfani da intanet a duniya.

A kowace rana ana yada bidiyon YouTube a cikin sa'oi biliyan daya yayin da Google, wanda shi ne mai shafin, yake taka rawa ta hanyar karfafa rumbunsa da makamashin da aka sabunta, kuma kallon wadannan bidiyon na fitar da hayaki mai gurbata muhalli a bangaren masu kallo.

Wani bincike da Jami'ar Bristol ta Birtaniya ta gudanar ya nuna cewa a shekarar 2016 mutane da ke kallon YouTube sun fitar da hayaki da ke gurbata muhalli kusan tan miliyan 11.13 - kwatankwacin yawan iskar gas da wani birni mai girman Glasgow ke samarwa, (inda ake gudanar da taron sauyin yanayi na COP26).

3. Tafkuna

Tafkunan ruwa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tafkuna

Lokacin da ruwa ya mamaye ƙasa don samar da tafki, tsirrai da duk wani nau'in halitta da aka nutsar da su sun fara ruɓewa tare da samar da iskar methane da ke gurbata muhalli - kwatankwacin abin da ke faruwa a cikin gonakin shinkafa.

Masu bincike daga Jami'ar Jihar Washington-Vancouver sun gano cewa tafkuna na duniya suna da alhakin kusan kashi 1.3 cikin dari na hayakin mai gurbata muhali da ake fitarwa a kowace shekara - daidai da adadin hayaƙin mai gurbata muhali da kasar Kanada ke fitarwa a jimilance.

Duk da haka, yawancin tafkuna kuma suna zama tushen madatsun ruwa.

Waɗannan su ne manyan hanyoyin sabunta wutar lantarki, ƙananan carbon da za a iya amfani da su a maimakon man fetur don haka za su iya magance hayakin methane da tafkunan da kansu ke samarwa.

Sai dai ana amfani da wasu tafkunan ruwa don samar da wutar lantarki.

4. Cukwi

Cukwi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Cukwi

Zai iya ba ku mamaki don sanin cewa cukwi shi ne na uku mafi girma da ke samar da hayakin mai gurbata muhalli a cikin nama da masana'antar madara bayan naman sa da rago.

Cukwi yana samar da kilogram 13.5 na hayaki mai gurbata muhalli daidai da kowane kilogram da ake ci, abin da ya sanya shi saman naman da ke haifar da sauyin yanayi irinsu kaza, naman alade, tolo-tolo ko kifi.

Ana amfani da kusan lita 10 na madara don samar da kilogiram ɗaya na cukwi domin hadashi, kodayake cukwi mai laushi ya ƙunshi ƙarancin madara, don haka yana da ƙaramin tasiri a kan muhalli.

Bangaren madara na duniya yana samar da kusan kashi hudu na iskar da ke gurbata muhalli wanda shanu da sauran dabbobin ke da alhakin a wani fanni, saboda suna fitar da methane mai yawa wanda, kamar yadda muka sani, yana yi wa yanayi illa fiye da hayaki mai gurbata muhali .

5. Ilimantar da yara mata

Wasu dalibai yara mata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ilimi na karfafa mata da yara mata wajen samar da muhalli mai inganci

Bincike ya nuna lokacin da mata da 'yan mata suka je makaranta kuma suna da damarmaki kamar maza, wannan yana ƙarfafa tsare-tsaren yanayi ta hanyoyi daban-daban.

Watakila macen da ta kammala karatun sakandare za ta haifi 'yaro guda a tsawon rayuwarta fiye da macen da ta kammala makarantar firamare.

Wannan raguwar yawan haihuwa yana da tasiri mai kyau a duniya ta hanyar rage yawan karuwar jama'a kuma wannan na rage yawan mutanen da ke fitar da hayaki mai gurbata muhalli.

Ilimi kuma yana bai wa mata da 'yan mata damar zama jagororin yanayi. Bincike ya nuna cewa kasashen da ke da yawan mata a majalisar dokokin kasar sun fi amincewa da yarjejeniyoyin muhalli na kasa da kasa, da samar da wuraren kariya da kuma samun tsauraran manufofin sauyin yanayi.

Farfesa Kimberley Nicholas wadda kwararriyace kan sauyin yanayi ta ce: "Ilimin mata da karfafawa a cikin al'umma yana da muhimmanci ga duniya amma ba kawai don sauyin yanayi ba ne mata da 'yara mata ya kamata su sami wannan damar - saboda duniya ce da nake son rayuwa a ciki."