An sako malamai da 'ya'yansu da aka sace daga Jami'ar Abuja

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni daga Najeriya sun nuna cewa 'yan bindigar da suka sace wasu malamai da 'ya'yansu daga Jami'ar Abuja sun sake su.
Wata sanarwa da Jami'ar Abuja ta fitar ranar Juma'a ta tabbatar da sako ma'aikatan nata da aka yi garkuwa da su ranar Talata.
Sanarwar, wacce shugaban jami'ar ya fitar, ta ce haɗin gwuiwar jami'an tsaron Najeriya da ta hada da sojoji da ƴan sanda da jami'an DSS ne suka ceto duka mutanen.
A ranar Talata ne 'yan bindigar suka kutsa kai rukunin gidajen Jami'ar da ke Gwagwalada da misalin karfe daya na dare suka malamai guda uku da 'ya'yansu biyu da kuma wani ma'aikacin Jami'ar.
Satar mutane domin karbar kudin fansa ta zama ruwan dare a arewacin Najeriya duk da ikirarin da hukumomi suke yi cewa suna bakin kokarinsu domin dakile ta.






