'Yan bindiga sun sace malamai da 'ya'yansu a Jami'ar Abuja

'Yan bindiga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bayanai sun nuna cewa 'yan bindigar sun ci karfin masu gadin Jami'ar sannan suka kutsa kai gidajen malamain suka sace su
An wallafa

Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu 'yan bindiga dauke da manyan makamai sun kai hari a Jami'ar Abuja, babban birnin kasar.

Wasu mazauna Jami'ar da ba sa so mu ambaci sunayensu sun tabbatar wa BBC Hausa cewa 'yan bindigar sun kutsa kai rukunin gidajen Jami'ar da ke Gwagwalada da misalin karfe daya na daren yau.

A cewar wani malami, an sace malamai guda uku da 'ya'yansu biyu da kuma wani ma'aikacin Jami'ar.

Bayanai sun nuna cewa 'yan bindigar sun ci karfin masu gadin Jami'ar sannan suka kutsa kai gidajen malaman suka sace su.

Rundunar 'yan sandan Abuja ta tabbatar wa aukuwar lamarin tana mia cewa mutum shida aka sace.

Ta ce ta baza jami'anta domin bin sahun 'yan bindigar da zummar kwato mutane da suka sace.

Satar mutane domin karbar kudin fansa ta zama ruwan dare a arewacin Najeriya duk da ikirarin da hukumomi suke yi cewa suna bakin kokarinsu domin dakile ta.