Shugaban sojojin Birtaniya na mamaki bisa zargin sojojinsa da kashe wata matashiya

Agnes na da shekara 21 aka kashe ta inda ta bar jinjira ƴar wata biyar

Asalin hoton, ROSE WANYUA

Bayanan hoto, Agnes na da shekara 21 aka kashe ta inda ta bar jinjira ƴar wata biyar
An wallafa

Shugaban sojojin Birtaniya ya bayyana cewa ya yi mamaki sakamakon zarge-zargen da ake yi cewa akwai yiwuwar sojojin ƙasarsa na da hannu a kisan wata matashiya ƴar ƙasar Kenya.

Janar Sir Mark Carleton-Smith, ya bayyana cewa a shirye yake domin tallafa wa hukumomi domin gano gaskiya kan batun kisan Agnes anjiru.

Ma'aikatar tsaron Birtaniya ta bayyana cewa tana aiki kafaɗa da kafaɗa da wani kwamitin bincike na ƙasar Kenya domin gano gaskiyar lamarin.

An gano gawar Ms Wanjiru a cikin wani tanki a wani otel a 2012 a garin Nanyuki mai nisan kilomita 200 daga Nairobi babban birnin ƙasar ta Kenya, kusan watanni uku bayan ta shafe dare guda tana holewa da wasu sojoji.

Sakataren tsaro na Birtaniya Ben Wallace, ya ce har yanzu ƙasarsa na jiran ji daga Kenya kan ko ta taimaka mata wajen gudanar da bincike wajen gano waɗanda suka kashe Ms Wanjiru.

Ms Wanjiru dai ta mutu ta bar jinjira ƴar wata biyar wadda a yanzu ƴar uwarta Rose Wanyua ke kula da ita.

Rose ɗin ta shaida wa BBC cewa ta haƙura dangane da batun yi wa ƴar uwarta adalci.

Rundunar ƴan sojin Birtaniya na da sansanin horaswa na din-din-din a Nanyuki da ke Kenya, kuma a ƙarƙashin wata yarjejeniya da gwamnatin Kenya, a duk shekara kusan bataliyar soji shida ke gudanar da atisaye na mako takwas a sansanin.

Ms Wanjiru dai ta bar karatun boko inda ta koma zaman kanta domin neman ƴan kuɗin da za ta kula da jinjirarta kuma ranar ƙarshe da aka ganta, ita ce ranar 31 ga watan Maris ɗin 2012, inda aka ganta ta fito daga wata mashaya a Nanyuki tare da wasu sojojin Birtaniya biyu.

Daga baya kuma aka ga gawarta a bayan wani ɗaki da sojojin suka zauna cikin tanki inda aka cire wasu sassan jikinta da kuma alamun yankar wuƙa a jikinta.

Alƙalin kotun Kenya Njeri Thuku ta yanke hukuncin cewa sojoji biyun nan na Birtaniya ne suka kashe matashiyar, inda alƙalin ta bayar da umarnin gudanar da bincike sai dai sojojin ba su yi komai ba, kamar yadda wata jaridar Birtaniya ta ruwaito.

Wani soja ya shaida wa jaridar cewa wanda ya aiwatar da kisan ya fito ya faɗa masa gaskiya kuma ya shaida wa sojojin amma kuma babu matakin da aka ɗauka.