'Yan Kenya da ke taimaka wa Turawa kan magudin jarrabawa

A graphic of a hand writing an essay while another hand takes it and offers cash.
    • Marubuci, Daga Reha Kansara da Ed Main
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Trending
  • An wallafa

Idan dalibi daga London ko New York ya hau kan intanet neman wanda zai biya ya rubuta masa jarrabawar rubutun zube, wanda zai samu cikin sauki shi ne dan kasar Kenya. Sashen BBC da ke bibiyar abin da ake yayi a intanet ya gano yadda ake samun mutanen Kenya da ke taimaka wa 'yan kasashen waje yin cuta yayin jarrabawa.

Kennedy yana yin aikin koyarwa amma sama da shekara biyar da suka gabata yana samun kudin da yake rayuwa ta wasu hanyoyin daban. "Ina rubutu irin na jami'a," in ji shi.

Tabbas yana cikin mutanen da suke gudanar da hada-hadarsu a intanet a fadin duniya, wani abu da yake tashe a Kenya. Sai dai Kennedy da wasu 'yan Kenya na kiran wannan tsari da "rubutun jami'a", amma sauran mutanen duniya na kiransa da cuta.

Idan kai dalibi ne ko kuma kana da dan da yake fama da aikin gida, kada ka samu wata damuwa domin kuwa Kennedy da sauran tawagarsa za su iya yi maka - a kan farashin da ya dace.

Za ka iya ba su aiki su yi kuma ya yi kamar kai ka yi da fatan ba za a kama ka ba.

Mutumin da ke shiga tsakani domin ganin wannan hulda ta kullu suna kiransa da "mai kawo abincin rubutun zube" wani shafi ne wanda daliban da ke cuta a karatu ke mika aikin da suke so a yi musu a ciki. Hoton da ake sanyawa a matsayin na mamallakin wannan shafi hoton wani kogi ne. Wanda ke nuni da cewa mutumin da zai yi rubutun ya fito ne daga Yammacin Afirka.

Kamar dai sauran masu yin irin wannan kasuwanci, hoton na karya ne ake sanyawa. Amma a maganar gaskiya mutanen Kenya ne suke yin wannan rubutun - yawanci ma kuma dalibai ne ke yi ko kuma wadanda suka gama jami'a.

Mafi yawan wadannan shafuka a Amurka suke ko kuma Gabashin Turai, kuma suna rage kusan rabin kudin da ya kamata mutum ya biya. Kudin kuma da ake biya ya danganta da saukin aiki a bangare daya kuma idan na digirin digirgir ne PhD yana fin tsada.

Anonymous rear shot of graduates wearing graduation robes

Asalin hoton, PA Media

Masu bincike da suka karanci harkokin kasuwanci na kiran wannan cuta da "kwantaragin cuta" suna cewa Kenya abar soyuwa ce ga kowa. Dalilinsu kuwa bayyane yake: Kenya na cikin kasashen da ke magana da Turanci a Afirka kuma tsarin karatunsu yana da matukar inganci, a gefe daya kuma matsalar tattalin arziki da matasanta ke fama da su.

Kennedy ya ce mutanen da ke fadi tashin rayuwa na ganin wannan sana'a ce da babu wanda zai yi watsi da ita.

"Nawa nake samu a matsayin malami, bai kai ya kawo ba idan ka kwatanta da abin da nake samu yanzu," in ji shi.

Malamin mai shekara 30 na samun kimamin $1360 a ko wanne wata, ya zarta mafi karancin albashin kasar da kadan.

Yaran da ke aiki tare da shi kan yi rubutu 200 a intanet duk wata.

Amma yaya yake ji idan aka kalli yadda yake taimakawa rugurgujewar ilimi a fadin duniya?

A matsayinsa na tsohon malami yana jin cewa "ba daidai ba ne abin da nake yi" amma yana aiki ne domin samun kudi. " Na damu amma abin da na fi damuwa da shi ai bai wuce rayuwata ba - a karo na biyu kuma sai a yi tunanin dacewarsa ko akasin haka," in ji shi.

David, a Kenyan academic writer with a mask working on a laptop.
Bayanan hoto, David yana samun kudin da yake karatunsa ne ta hanyar rubuta wa wasu jarrabawa

David na daya daga cikin yara 10 da ke shekarar karshe a jami'a wanda ya ce yana daukar nauyin karatunsa ne ta wannan hanya.

"Iyayena ba za su iya biya min kudin makaranta ba," a cewarsa. "Sai na fara tunanin yadda zan dauki nauyin kaina na kuma taimaka wa iyayena."

Shekara biyu da suka gabata, za a iya cewa David ya samu nasa digrin ne ta hanyar yi wa abokan huldarsa na Amurka da na Birtaniya rubutu kusan 360.

Yana samun kudin da suke isarsa ya yi hayar gonar da zai noma a kauyensu, ya dauki 'yan kwadago sun yi masa aiki - wanda ya ce hakan tanadi yake yi wa gobensa.

Wannan irinta ce hanyar da daliban da ke cuta ke rudar kansu da ita. Suna ganin sun samu rubutun da aka yi musu komai ya wuce. Amma a zarihin gaskiya wani ne ya yi aikin kuma shi ne zai samu kyakkyawan sakamakon yin shi duk dadewa.

"Na sayi safukan masu irin wannan sana'ar tamu sama da 10", in ji Kennedy. "Wani ma na saye shi sama da dalar Amurka 4550. Bayan wannan babu wata hanyar samun abokan hulda.

Samun irin wadannan shafukan na daga cikin abubuwan da David ya mayar da hankali a kansu bayan kammala jami'arsa. A shekara 23 amma har ya fara samar da wadanda ke kwaikwayons. Yana horas da matasa domin shiga irin wannan sana'a. "A cikin wannan harka muna samun abokai kuma muna taimakawa juna. Don haka yanzu ta zama wata masana'anta da ke tasowa."

Wasu kuma ba su da wani cikakken kwarin gwiwa kan wannan aiki. John ya shiga wannan aiki bayan kammala digirinsa. Amma yana fatan barin harkar da zarar burinsa ya cika na yin aiki a kafafen yada labarai.

"Akwai mutanen da ke yin aikin a bangaren jinya. Ba zan so watarana a kaini wajen wanda wani ya yi wa jarrabawa ba ya biya shi. Kasan abu ne mai matukar hadari. "

Dr Gladys Nyachieo, ta sashen koyar nazarin halayyar dan adam da ke jimi'ar Nairobi. ta yi amannar cewa hakkin shawo kan wannan matsala ya rataya ne a wuyan kasashen da ke da wadata wadanda dalibansu ne abokan huldar. Idan ba su kawo ba ai ba za a yi wannan harkallar ba.

Dr Gladys Nyachieo

Asalin hoton, Multimedia University

Bayanan hoto, Dr Gladys Nyachieo ta ce kasashe masu arziki ne ya kamata su dauki mataki kan wannan harkalla.

"Idan za su iya wani abu akai na mayar da shi saba doka ina ganin zai iya rage abun," in ji ta.

A gefe guda Dr Nyachieo na nata kokarin domin ganin an kawo karshen haka.

"Na gaya wa dalibaina bai kamata ba ya saba ka'ida. Amma dai shi ne kawai abin da zan iya."