Zaɓen Nijar 2020: Za a je zagaye na biyu saboda babu jam'iyyar da ta ci kashi 50

Hukumar zaɓen Nijar CENI ta tabbatar da cewa za a je zagaye na biyu a zaɓen shugaban ƙasar Jamhuriyar Nijar, wanda aka gudanar ranar 27 ga watan Disamban 2020.
Shugaban hukumar Barista Isiaka Sunna ya ce an cimma matakin ne saboda babu jam'iyyar da ta ci kashi 50 ko fiye na ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen.
Kamar yadda jadawalin hukumar zaɓe ya nuna, ranar 21 ga watan Fabarairun 2021 ne za a gudanar da zagaye na biyun.
Sakamakon zaɓen da CENI ta bayyana yanzu ya nuna cewa ɗan takarar jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarraya, Bazoum Mohamed, shi ne ya lashe kashi 39,33 cikin 100, inda yake da kuri'a 1, 879, 000.
Sai kuma Mahamane Ousmane na jam'iyyar RDR Canji da ya lashe kashi 16.99 cikin 100 kuma ya samu ƙuri'a 811,838.
Hakan na nufin za a fafata zaɓen zagaye na biyu tsakanin 'yan takarar guda biyu, waɗanda su ne kan gaba a zagayen farko.
Za a fara yaƙin neman zaɓen a zagaye na biyu daga ranar 29 ga watan Janairun 2021 zuwa 19 ga watan Fabarairu.
Tun bayan fara mulkin demokuraɗiyya a Nijar ranar 29 ga Yulin 1991, sai an je zabe zagaye na biyu kafi a samar da shugaban ƙasa.
Wasu daga cikin jam'iyun siyasar kasar kan goyi bayan ɗan takarar da ya zo na daya, wasu kuma su goyi bayan wanda ya zo na biyu. Wadanda suka yi rinjayen ƙuri'u a zagaye na biyu ne za su kafa gwamnati.










