Zaɓen Nijar: 'Yan takara 30 na fafatawa don karɓar mulki daga Issoufou

Asalin hoton, Getty Images
'Yan takara 30 ne ke fafatawa da juna don karɓar ragamar mulki daga Shugaba Mahamadou Issoufou, bayan ƙarewar wa'adinsa biyu tsawon shekara goma.
Zaɓen shi ne irinsa na farko da wani zaɓaɓɓen shugaban ƙasa zai miƙa mulki cikin ruwan sanyi ga wani takwaransa da za a zaɓa.
Kuma ko ma wane ne zai zamo sabon shugaban Jamhuriyar Nijar a Lahadin nan, zai fuskanci ƙalubala iri daban-daban ciki har da taɓarɓarewar tsaro da cin hanci da rashawa da kuma talauci.
Za a fara kaɗa ƙuri'a ne da ƙarfe 08:00 agogon Nijar a rufe da ƙarfe 07:00 na dare.
Shugaban CENI a jihar Damagaram, Mai Shari'ah Shebu Musa ya ce sun samu kayan aiki da wuri, kuma sun ɗauki matakai na ganin an fara zaɓen a kan lokaci, ba tare da samun tsaiko lokacin da ake gudanar da zaɓen ba.
"Mun ɗauki matakai ƙwarara, don ganin haka ba ta faru ba. Don haka muna da kyakkyawan zaton cewa ba za a samu wata matsala ba," in ji shi.
Mutum fiye da miliyan bakwai za su fita zabe
Daga cikin mutane fiye da miliyan bakwai da ke kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen har da ɗumbin matasa da suka kai shekarun yin zaɓe, kuma suka zaƙu don fid da shugaban Nijar na gaba.
Suna dai fatan shugaban mai zuwa zai kawo gagarumin sauyi a rayuwarsu ta hanyar bunƙasa ilmi da harkokin kula da lafiya da kuma samar da aikin yi.
Wani matashi mai suna Suleiman Ibrahim a jihar Damagaram ya ce yana jin daɗi sosai ganin lokaci ya yi da shi ma ƙuri'arsa za ta yi tasiri wajen nema wa ƙasarsa mafita.

Asalin hoton, @Mohamed Bazoum
Cikin 'yan takara 30 ɗin da ɗayansu zai gaji Mahamadou Issoufou har da Mohamed Bazoum, na jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya.
Daɗaɗɗen ɗan siyasar mai shekara 60, ya riƙe muƙamin ministan cikin gida tsawon shekara huɗu a baya, kuma abokin ƙawance ne mai alƙawari ga Shugaba Issoufou.
Karon farko ke nan yake takarar shugaban ƙasa a Jamhuriyar Nijar.

Asalin hoton, Getty Images
Akwai kuma, Mahamane Ousmane, zaɓaɓɓen shugaban Nijar na farko da ya hau mulki a 1993.
Sai kuma Seini Oumarou, tsohon Fira ministan Shugaba Tandja Mamadou, shi ma yana takara.
Dukkansu sun ƙuduri aniyar warware matsalar tsaro a matsayinta na ko tantama babu, ta zama babban ƙalubalen da shugaba mai jiran gado zai fuskanta.
Hare-haren ta'addanci wata babbar barazana ce musamman a yankunan kan iyaka da Najeriya.

Asalin hoton, Getty Images
'Batun tsaro shi ne ya fi damun mu'
Hukumomin zaɓe a jihar Diffa sun ce batun tsaro shi ne muhimmin al'amari a lokacin wannan zaɓe, don haka suke kira ga jama'a su taya jami'an tsaro lura.
Mamman Aminu Kundi, shugaban hukumar CENI a Diffa ya ce ta hanyar aiki tare tsakanin jama'ar jihar da jami'an tsaro da kuma malaman zaɓe, ana iya daƙile duk wata matsala da ka iya tasowa cikin gaggawa.
"Kiranmu ga al'umma shi ne su ƙara buɗe ido, su ƙara buɗe kunnuwa. Dukkan abin da suka gani, ya zan kasance mai ruɗani, ko wanda ma suke shakku, ya kamata su isar da saƙon ga mahukunta," in ji Kundi.
An tura masu sa-ido na cikin gida 5,563 da kuma masu sa-ido na ƙasashen duniya 939 don bibiyar yadda zaɓukan na Lahadi za su kasance.
Zaɓen zai kasance wani muhimmin zango cikin tarihin siyasar Nijar, a matsayinta na ƙasa wadda ta fuskanci katsewar mulkin dimokraɗiyya har sau uku.
Yanzu kuma a karon farko tana shirya miƙa mulki zuwa hannun wata zaɓaɓɓiyar gwamnatin farar hula tun bayan samun 'yancin kai.
Nijar dai na cikin ƙasashe mafi talauci a duniya kuma tana ci gaba da zama mai rauni bisa la'akari da yawan alƙaluman fatara na kashi 41.4% da ke addabar fiye da mutum miliyan 9.5.









