ISWAP ta kashe sojojin Najeriya biyar a Borno

Asalin hoton, BOKO HARAM
Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce ƙungiyar ISWAP ta kai harin kwanton ɓauna ga kwambar motocin sojin Nijeriya, inda ta kashe soja biyar, tare da sace fararen hula.
Ya ce an far wa kwambar motocin sojin ne ranar Asabar, kwana guda bayan 'yan ta-da-ƙayar-bayan sun auka wa matafiya a wannan yanki, tare da sace mutum 35, bayan kashe wata mata.
Harin na ranar Asabar a wajen Mafa, shi ne na baya-bayan a hare-haren da 'yan ta-da-ƙayar-bayan suka kai cikin ƙarshen makon jiya a jihar Borno da ke arewa maso gabas.
Ko a ƙarshen makon da ya wuce masu ikirarin jihadin sun sace matafiya 35 a babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.
Wadanda abin ya faru a kan idonsu sun ce, marahar sun sanya shinge ne irin na jami'an tsaro suka riƙa fito da mutane daga motocinsu, kuma suka harbe wata mace guda har lahira.
Hare-hare da garkuwa da mutane na ƙara zafafa a arewacin Najeriya, duk da iƙirarin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na cewa tana cin galaba kan yaki da masu ta-da-ƙayar bayan.
Kuma harin baya-bayannan da ya fi jan hankali har ya janyo kakkausar suka ga gwamnati shugaba Buharin shine na yankin Zabarmari a jihar Borno da ke arewa maso gabas, a lokacin da mayaƙan ƙungiyar Boko Haram suka dira yankin, suka kashe manoma 42,
Majiyar majalisar dinkin duniya ta ce wadanda kungiyar ta yiwa kisan gillar a Zabarmari sun haura mutum 100.
Ko a makon da ya gabata mahara sun sace 'yan makarantar sakandaren kwana da ke garin ƙanƙara su sama da 300 a jihar Katsina da ke arewa maso yamma, duk da an yi nasarar karbo su a karshen makon.
Ko shekaran jiya Asabar yan bindiga sunyi yunƙurin sace wasu mata ƴan makarantar Islamiyya su 80 a garin mahuta duk dai a jihar ta Katsina, wadda ita ce mahaifar shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari.










