Zaɓen Amurka na 2020: Muna samun hadin kai daga Shugaba Trump – Biden

Zaɓaɓɓen shugaban Amurka Joe Biden, ya ce kwamitin karɓar mulkinsa na samun cikakken hadin kai daga gwamnatin Shugaba Trump, bayan amincewa da nasarar da ya samu a zaben shugaban kasar da ya gabata.
Yayin wata hira da kafar talabijin din NBC, Mista Biden, ya ce suna samun sahihan bayanai dangane da sha'anin tsaron kasar da kuma abin da ya shafi annobar korona.
Sai dai ya ce har yanzu bai yi wata magana da Shugaba Trump ba, wanda ke ci gaba da musa cewa ya sha ƙasa a zaɓe.
Zaɓaɓɓen shugaban kasar ya gabatar da wasu daga cikin jami'an gwamnatinsa, yayin da ya bayyana cewa ''Amurka ta dawo don ci gaba da jagorancin duniya''.
Mene ne saƙon Mista Biden?
Da yake magana da tashar NBC a shirinta na Labaran Dare, Biden ya tabbatar da cewa har yanzu bai yi magana da shugaban ƙasar ba amma ya ƙara da cewa bai yi zaton za a samu ɓata lokaci wajen miƙa mulki a farkon wa'adinsa ba.
"Ana tafiyar hawainiya amma dai an fara kuma akwai sauran wata biyu nan gaba, don haka ina jin daɗi kan yadda za mu iya cimma hakan," in ji shi.
Ya ce akwai shirin ganawarsa da tawagar da ke kula da Covid-19 na Fadar White House kan rarraba allurar riga-kafi.
Sannan kuma yana samun bayanai na duk rana kan ci gaba da matsalolin da ake samu dangane da ƙasashen duniya - a yanzu Mista Biden na iya ganawa da manyan jami'an gwamnati sannan zai iya sarrafa miliyoyin daloli a yayin da yake shirin karɓar mulki a ranar 20 ga watan Janairu.
Biden, wanda tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne ƙarƙashin Barack Obama ya ce wannan mulkin ba zai zama "karo na uku na mulkin Obama ba" saboda al'amuran duniya a yanzu sun sha bamban da na lokacin mulkin Obama da Biden na baya.
"Amurka ta dawo" kuma a shirye take ta jagoranci duniy, babu ja da baya kan haka," ya faɗa a lokacin da ya gabatar da tawagar gwamnatinsa a ranar Talata a Wilmington da ke Delaware.











