Zaɓen Amurka na 2020: Abin da sabon tsarin Biden kan ƙasashen waje ke nufi a garemu

Asalin hoton, Reuters
Mutane ukun da zababben shugaban Amurka Joe Biden su jagoranci tawagar harkokin manufofin kasashen wajensa, da za su bayar da gudumawar irin gogewar da suka samu a shekaru da dama a Fadar White House, amma kuma suna fuskantar suka daga wadanda ke adawa da hakan, idan aka hada da shekarun da suka shafe suna aiki a cikin gwamnatin Amurkar.
Ga kadan daga abinda ke nuni da ko su wanene su, da kuma abinda masana ke cewa game da sakon da Mista Biden ke aikewa tare da zabinsa na manyan jami'an diplomasiyyar.
Su wane ne su?
Mutane ukun da za su riƙa bai wa Mista Biden shawara kan al'amuran da suke wajen Amurka ba sanannu ba ne a wajen Washington.
Antony Blinken, Linda Thomas-Greenfield da Jake Sullivan dukkaninsu tsofaffin ma'aikatan ofoshin hudda da kasashen waje ne.
Mista Blinken, mai shekaru 58 - wanda ya yi aiki da Mista Biden shekara 20 da suka gabata - an dauko shi ne don ya yi aiki da sakataren harkokin waje , babban jami'an hulɗar diflomasiayya na kasar.
Linda Thomas-Greenfield, daya daga cikin ƙusoshi mata bakaken fata da ta shafe shekaru tana aiki kan harkokin kasashen Afirka, an dauko ta ne ta yi aiki da jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya.
Jake Sullivan tsohon ma'aikacin sashen hulɗa da kasashen waje ne kuma mai bai wa Hillary Clinton shawara ne, wanda ya taka muhummiyar rawa a fannin zama teburin tattaunawa kan yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran a shekara ta 2015.
Ya yi aiki a matsayin mai bai wa Mista Biden shawara kan harkokin tsaron kasa.
'Yan cikin gida
Mr Blinken ya yi aiki da Mista Biden har na tsawon kusan shekaru 20, lokacin da Mista Biden din ya riƙe kwamitin harkokin hulɗa da kasashen waje na majalisar dattawan Amurka.
Wasu masu suka sun dora masa alhaki da hannu wajen matakin da Biden ya dauka na kada kuri'ar kai hari a kasar Iraƙi a shekara ta 2003.
Wannan dangantaka za ta yi amfani wa tawagar sosai, na tsofaffin jami'an diflomasiayyar Amurka, amma kuma hakan na nufin rashin samun ra'yoyi mabanbanta kenan.
Haka kuma irin gogewarsu a Washinton a matsayinsu na tsofaffin jami'ai kan manufofin kasashen waje ba za ta kara musu wani tagomashi ba ko kadan'' - daidaikun mutane a gwamnati da yake kallon suna kokarin yi masa zagon kasa kan ajandarsa.
Wannan ba tawagar masu adawa da juna ba ce. A yayin da suke da tarihin taba yin aiki mai kyau tare, za kuma su samar da gamsassun bayanai da shawarwari a teburin dakin shawara, da kuma irin gogewar da suke da ita a fannin da ya shafi tashe-tashen hankula a kasashen duniya.
"Su ba zababbun 'yan siyasa bane a kasar, amma kuma za su taimaka wajen jagorantar muhimman abubuwa na Amurka. Su masu daukar mataki ne cikin gaggawa, ba masu tsaurarawa ba ne," a cewar PJ Crowley, tsohon mataimakin sakataren harkokiin wajem Amurka.
Daukarsu aiki na nuni da dawo da al'amura kan daidai da kuma kawo karshen yadda ake yi wa manufofin gwamnati hawan kawara.
"Amma abin tambaya a nan shi ne dawo da komai kan daidai ya isa. Tawagar ta yi amanna da martaba da kasaitar Amurka wanda hakan ka iya haifar da yin amfani da karfin soja da ya wuce kima," Andrew Bacevich, shugaban cibiyar Quincyfor Responsible Statecraft.
A matsayinta na wadda ta dade tana aiki a fannin harkokin waje, Mrs Thomas-Greenfield, na wakiltar '' bangaren gwamnati'' wanda Trump ke dauka a matsayin maras amfani.
"A ganin Donald Trump, jami'an huldar difilomasiyya ne kashin bayan bullo da dabatun 'yancin kasa da kasa da ya ke son ya rushe. Wannan shi ya sa a yanzu haka batun karfafa guiwa ya ja baya a ofishin huddar jakadanci," Charles Kupchan, tsohon mamba na kwanmitin tsaron kasa a fadar White House.

Asalin hoton, Getty Images
Kawancen kasashen waje
Ajandar farko ta tawagar Mista Biden za ta kasance sake shiga kawance da kuma alaka da kungoyoyi, kawance da yarjejeniyar da Mista Trump ya dade yana kokarin kassarawa a cikin shekaru hudu da suka gabata.
Za a dora musu nauyin dawo da Amurka cikin yarjejeniyar Paris ta sauyin yanayi tare da saka Amurka cikin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).
Za kuma su bi diddigin batun yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran, dinke dangantarka da kungiyar tsaro ta NATO tare da neman yarjejeniyar kasuwanci don rage wa kasar China tagomashin da ta ke kara samu.
Daya daga cikin dalilan da suka saka aka zabi Trump shi ne saboda Amurkawa da dama sun yi imanin cewa manufofin gwamnatin Amurka kan kasahen waje sun gaza. Abin tambaya a nan shi ne, ko wannan tawaga ta koyi isasshen darasi kan sauye-sauyen da muke ainihin bukata da suka hada da rage kasafin kudaden rundubar sojin kasar da kuma rage yawan amfani da karfin soj?Andrew Bacevich
Donald Trump ba taba kafa tawagar tsaron kasa ba. A maimakon haka, ya ci gahin kansa a yayin da ya kewaye kansa da 'yan kwangila masu zaman kansu da zai iya dauka aiki ya kuma kore su a duk lokacin da ya ga dama shafinsa na twitter. Duka wadannan jami'ai uku sun yi aiki a ofishin hudda da kasashen wajen Amurkar kuma za su kara bayar da sabuwar muhimmiyar gudumawa kan huddar diplomasiyyar kasa dakasa, da kuma hadin guiwa wajen shawo kan matsalolin annoba, sauyin yanayi da kuma na kalubalen kasar China. PJ Crowley
"Babban kalubalen zai kasance shawo kan 'yan kasashen waje, abokan hudda da kasashe aminai cewa Amurka na da martaba a fannin karfin ikonta - cewa ''Amurka ta dawo'' kamar yadda zababben shugaban kasar ke cewa. Gwamnati mai jiran gado na da aniyar farfado da dangantaka da ta yi tsami tsakaninta da kwayenta da ta dogara da su fiye da shekaru saba'in da suka gabata," in ji Stewart Patrick, daraktan cibiyar harkokin kasa da kasa da kuma shirin harkokin tafiyar da mulki da kasashen duniya.

Asalin hoton, Fadar White House
Dawowar kwararru?
Akasarin kwararru sun amince cewa tawagar da Mista Biden ya tanada ta fi gogewa fiye da wadanda Mista Trump ya zauka, kamar sakataren harkokin wajensa na farko Rex Tillerson, wanda tsohon shugaban kamfanin mai na Exxon Mobil ne.
Amma kuma gadon da Mista Trump ya bari a ofishin huldar jakadanci - da ake kallon tarin jami'an huldar diplomasiayya da ba su da tarbiyya, sun yi murabus a lokacin, kana wanda ya gaje shi Mr Tillerson Mike Pompeo - ya yi nisan da ba za a iya tankwara shi ba a dare daya.
Charles Kupchan ya ce: "An yi ta samun ficewar kwararru da gogaggu daga ofishin a karkashin Tillerson da Pompeo. Nuna karfin iko a ofishin huddar diplomasiyyar ya kasance maras iyaka. Galibi manufofi kan kasance daga kasa, kuma sai sun kai ga teburan hukumomi da dama kafin su kai ga shugaban kasa. Hakan bai tana faruwa na a lokacin Trump."
PJ Crowley ya ce: "Suna samun bayanai akai akai game da kasashen duniya. Sun kuma yadda sosai kan shugabancin Amurka da kwancen kasa da kasa. Dukkaninsu ukun sun yi aiki a ofsihin huddar da kasashen waje da kuma hadin kai waje n shwao kan matsalar annobar da ta shafi duniya da gaggawa, zauwa sauyin yanayi da kalubalen kasar China."
(Rahoton Tara McKelvey da Max Matza)











