Gasar kofin duniya 2026: Me kuke son sani kan wasan Faransa da Senegal?

Takaitaccen Bayanin Wasa

Gasar Kofin Duniya
- Matakin rukuni
France versus Senegal kick off 20:00
Faransa
20:00
plays
Senegal

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu tare da taimakon AI

Gasar kofin duniya 2026: Me kuke son sani kan karawar Faransa da Senegal?, Gasar kofin duniya 2026

Liv

Asalin hoton, Getty Images

Tawagar Faransa da ta Senegal za ta kece raini a wasan farko a gasar cin kofin duniya a rukuni na tara ranar Talata.

Shi ne wasan farko da za a buga a rukunin a Amurka, amma karo na biyu da Faransa da Senegal za su buga gasar kofin duniya, bayan 2002 da Senegal ta ci 1-0 a Korea/Japan.

Faransa, wadda za ta buga gasar cin kofin duniya karon farko a Amurka na fatan ta kai zagayen karshe karo na uku a jere - bayan lashe kofin 2018 a Rasha da rashin nasara a hannun Argentina a 2022 a Qatar.

Senegal, wadda take da fitattun ƴan wasa a faɗin duniya, wadda ta lashe kofin Afirka Afcon daga baya aka bai wa Morocco, ta kai zagayen ƴan 16 a Qatar a 2022.

To sai tawagar Senegal za ta fuskanci kalubale na rashin magoya bayanta da yawa, sakamakon da gwamnatin Amurka ta hana su izinin shiga kasar, kenan sai dai waɗanda ke Amurka su mara mata baya.

A lokacin da Faransa da Senegal suka kara a 2002, Faransa ce mai rike da kofin da kuma na Fifa Confederation Cup da ta ɗauka a 2001, saboda haka sai aka yi hasshen za a yi tafiyar ruwa da Senegal a karawar.

To sai dai kuma ba a nan gizo ke saƙa ba, domin Senegal ce ta yi nasarar cin 1-0 a wasan ta hannun Papa Bouba Diop. Har yanzu ana tuna wasan da kalubalen da Faransa ta fuskanta a fafatawar.

A wancan lokacin da suka fara haɗuwa, kociyan Senegal na yanzu, Pape Thiaw yana buga wa kasarsa tamaula a shekara 24 baya a lokacin da Senegal ta yi nasarar doke Faransa.

Saboda haka a yanzu kociyan ya shirya jan ragamar kasar, domin ta taka rawar gani a wasannin bana da za a gwabza tsakanin tawaga48 a karon farko a tarih.

Wasu ƙididdiga da ya kamata ku sani

Wasa: Gasar cin kofin duniya 2026 da ake yi a Amurka da Kanada da kuma Mexico

Tsakani: Faransa da Senegal

Ranar wasan: Talata 16 ga watan Yuni 2026

Filin wasa: New York New Jersyey, Amurka

Lokacin da za a buga wasan: Karfe 8:00 pm agogon Najeriya da Niger

Haɗuwa tsakaninsu: Karo na biyu da za su kara a kofin duniya, bayan 2002 da Senegal ta ci 1-0.

Liv

Asalin hoton, Getty Images

  • Duk abin da ya kamata ku sani kan Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026
  • An raba maki tsakanin Brazil da Morocco
  • Gasar kofin duniya 2026: Ghana ta bukaci a duba dalilin hana Partey shiga Kanada

Me kociyoyin suka ce kafin karawar?

Didier Deschamps, kocin Faransa:

"Fara kowacce gasa da kwarin gwiwa abu ne mai kyau da muhimmanci, domin wannan shi ne wasan farko a rukuninmu. Koda yake ba za a ce wannan wasa ne da zai yanke hukunci kan makoma ba, saboda har yanzu akwai sauran wasanni biyu da za a buga daga wannan (a rukuni). Ko a ƙididdiga ma, zakaran kofin duniya na baya da ya wuce ya sha kashi a wasansa na farko. Amma hakan bai hana shi zama zakaran duniya ba daga baya.

Duk da haka, mafi kyawun yanayi shi ne ka fara da nasara a rukunin da ke a karawar farko mai tawaga huɗu. Wannan ne ko da yaushe burinmu yayin da muke tunkarar wasan farko."

Pape Thiaw, kocin Senegal:

"Shin zai zama abin mamaki idan Senegal ta doke Faransa? A gare ni, a'a. Domin muna da ƴan wasa da suke taka leda a manyan mataki a fitattun ƙungiyoyi a duniya. Mun samu tikitin shiga Kofin Duniya sau uku a jere kenan. Haka kuma a gasar Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) ta baya-bayan nan, mun kai wasan ƙarshe sau uku cikin gasa huɗu.

Don haka, a gare ni, ba zai zama abin mamaki ba don mun ci Faransa. Na san irin ƙoƙarin da tawagarmu ke yi. Muna ɗaukar wasa ɗaya bayan ɗaya. Za mu kara da kasa mai ƙarfi sosai, musamman idan aka yi la'akari fitattun ƴan wasanta da irin ƙarfin tawagogin da ke a cikin rukuninmu.

Wannan Kofin Duniya ne, kuma na yi imani cewa kowace kasa ta cancanci kasancewa a nan. A ƙwallon ƙafa, ba na son magana kan yin abin mamaki. Kowacce kasa ta yi aiki tuƙuru domin isa wannan mataki, kuma za mu fuskanci kowanne wasa da burin samun nasara."

Filin da zai karɓi bakuncin wasan

Liv

Asalin hoton, Getty Images

Filin wasa na New York New Jersey shi ne zai karbi bakuncin wasan karshe a gasar cin kofin duniya 2026.

Ya gudanar da babban wasa a ƙwallon zari rugar Amurka wato tsakanin National Football League tsakanin New York Giants da New York Jets, haka kuma ya shirya fafatawa a wasan karshe a 2016 a Copa America Centenario, inda Chile ta doke su Lionel Messi da Argentina a bugun fenariti.

Fitattun mawaka sun baza basirarsu a filin New York New Jersey daga ciki har da Bruce Springsteen da Beyonce da Ed Sheeran da kuma Taylor Swift.

A katafaren filin ne aka buga wasan karshe a FIFA Club World Cup 2025, inda Chelsea ta doke Paris St Germain 3-0 ta lashe kofin karkashin koci, Enzo Maresca.

Shi wannan filin zai karɓi bakuncin wasa biyar a cikin rukuni a gasar cin kofin duniya a bana da guda ɗaya a zagayen kwata fainal.

Liv

Asalin hoton, Getty Images

Ƴan wasan da ake sa ran fara wasan da su

Ƴan wasa 11 daga Faransa:

Maignan; Kounde, Saliba, Upamecano, Hernandez; Tchouameni, Rabiot; Olise; Mbappe, Dembele, Doue

Ƴan wasa 11 daga Senegal:

E. Mendy; A. Mendy, Koulibaly, Niakhate, Diouf; Matar Sarr, P. Gueye, L. Camara; I. Sarr, Jackson, Mane