Me ya sa wasu ƴan Najeriya suka wawushe kayan abincin tallafin korona?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Nduka Orjinmo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
An ci gaba da wawaso a Najeriya, yayin da mutane suka kai farmaki tare da fasa manyan daƙunan ajiyar kayan abinci na gwamnati, inda aka ajiye kayayyakin tallafin kullen korona a Abuja babban birnin tarayyar kasar tun a ranar Litinin.
Farmakin a Gwagwalada, da ke wajen babban birnin, shi ne na baya-bayan nan da aka kai, wanda suka biyo bayan tashe-tashen hankula masu nasaba da zanga-zangar END SARS da suka faru a kasar.
Masu wawason sun arce da buhunan shinkafa da sukari da kwalayen taliyar yara, da sauran kayan masarufi.
Mahukuntan dai sun musanta cewa sun ɓoye kayan ne don sun raba wa iyalai da abokansu.
Me yasa aka ɓoye kayan tallafin?
Gwamnonin jihohi sun sanar da cewa sun ajiye kayan ne saboda mutanen da ke cikin halin matsi a cikin al'umma, da kuma shirin ko ta kwana saboda yiwuwar ɓarkewar annobar karo na biyu.
Sanarwar ta su na yin nuni da cewa akasarin jihohin na jiran lokacin da za su ƙaddamar da rarraba kayyakin, wanda ke nuna hakan a matsayin cikin ƙasaitaccen biki.

Asalin hoton, Getty Images
Amma kuma galibi waɗanda ba su taba samun tallafi daga gwamnatocin ba a cikin watannin da aka shafe ana kulle saboda guje wa yaɗuwar annobar korona, ba su gamsu da waɗannan bayanai ba.
Kullen dai ya dakatar da miliyoyin mutane fita neman abinci.
Kana, gano wasu kayan tallafin na korona a gidajen wasu manyan 'yan siyasa ya sake shafa wa gwamnatocin kashin kaji.
Wani ɗan siyasa a jihar Lagos, ya ce yana shirin raba kayayyakin ne a bikin zagayowar ranar haihuwarsa - kwanaki biyu bayan da masu wawason suka kai samame gidansa.
An dai zargi gwamnatin tarayya da yin almubazzaranci da kuɗaɗen tallafin, da galibi wasu masu hannu da shuni na ƙasar ne suka bayar da gudunmawa.
Sai dai, daya daga cikin 'ya'yan shugaban kasar, Zahra Buhari ta wallafa a shafinta na Instagram cewa gano kayayyakin tallafin da aka yi a manyan ɗakunan ajiyar gwamnati, da ba a raba wa jama'a ba ya nuna cewa mahaifinta ya yi amfani da waɗannan kuɗaɗe yadda suka kamata.
"Yanzu da yake mutane sun gano cewa (Shugaba Muhammadu) ya rarraba isassun kayyakin tallafi a faɗin kasar, a bayyane take cewa Buhari ba shi ne matsalarmu ba,'' ta wallafa.
Shin yaya girman wannan wawason kayan tallafi?
Akasarin jihohin Najeriya da manyan biranensu sun shaida wannan farmaki da wawason kayan tallafin a ɗakunan ajiyar gwamnatin har ma da na ɗaiɗaikun mutane.
Wasu sun rasa rayukansu wajen turmutsutsu, bayan da mutane suka maƙare manyan ɗakunan ajiye kayan tallafin, a wani gefen kuma saboda nauyin buhunan abincin mai nauyin kilo 50.

Asalin hoton, Getty Images
Mahukunta a jihar Adamawa arewacin Najeriyar sun shaida wa BBC cewa mutane biyar ne suka mutu a turmutsutsu lokacin da ake kwasar ganimar a ɗakin ajiyar kayan da ke can.
Wasu gwamnonin jihohin sun kafa dokar hana fita ba dare ba rana domin daƙile farmakin, yayin da a ranar Lahadi babban sifeton 'yan sandan ƙasar ya umarci jami'ansa da suka kawo ƙarshen tarzomar.
Mutane fiye da 400 ne aka cafke a birnin Lagos kaɗai, kuma za a gurfanar da su kamar yadda hukumomin suka bayyana.
A birnin Calabar da ke kudancin ƙasar, gwamnatin jihar ta bayar da umarni ga jami'an tsaro da su gudanar da samame gida-gida don binciko waɗanda suka yi wawason kayan.
Wannan yana da nasaba ba zanga-zangar ta #EndSars ne?
Masu wawason ba masu zanga-zangar lumana ba ne da ke neman a kawo ƙarshen cin zalin da 'yan sanda ke yi da suka fara a farkon wannan watan, amma abin da ke faruwa a yanzu ci gaban karya doka da oda ne bayan da wasu 'yan daba suka yi kutse a cikin zanga-zangar.
Masu zanga-zangar sun yi zargin cewa 'yan sanda da ke wurin suna kallo a lokacin da 'yan dabar ke kai musu farmaki a birane Lagos da Abuja.

Wasu labaran da za ku so ku karanta:

A wani ɓangaren kuma, wani faifen bidiyo ya nuna cewa jami'an 'yan sandan ne suka ƙarfafa wa 'yan dabar gwiwa su kai wa masu zanga-zangar hari, da ya haddasa mutuwar wasu da kuma jikkata wasu.
Nuna halin ko in kula daga jami'an tsaron, ya sa suka ci gaba da cin karensu babu babbaka suka toshe manyan hanyoyi, tare da lalata wa da ƙona shagunan jama'a, kafin su kai farmaki a manyan ɗakunan ajiyar da ke maƙare da kayan tallafin.
A ɗaya faifen bidiyon da aka wallafa a shafin yanar gizo, ana iya kallon mutane a wani wuri suna sasantawa da jami'an soji na su yi wawason kayan cikin lumana a wani ɗakin ajiyar kayyyakin da ke jihar Kwara, inda jami'an sojin da ke lura da dakin ajiyar suka shaida wa masu kwasar ganimar da su rika bi sa sannu yayin da suke kwasar ka
Su wanene ke wawason kayan?
Akasari matasa ne, da ke da ƙarfin iya hawa saman dalar buhunan shinkafar da sauran kayayyakin su kuma ɗaga su a lokaci guda.
A wasu wuraren masu ƙaramin ƙarfi da tsofaffi sun shiga cikin taron masu ɗibar ganimar a ɗakin ajiyar kayayyakin.

Asalin hoton, Getty Images
Mutane da dama sun cika da mamaki da gano wuraren ajiyar kayan tallafin gwamnatin, da ba abu ne da aka cika sani ba.
Amma kuma lokutan gano waɗannan wurare da kuma fitar ɗangon da dubban jama'a suka yi ya nuna akwai alamun abin an tsara shi ne.
Shin yaya mutane ke kallon wannan lamari?
Wannan ya zama wani darasi ga wasu mutane.
Wasu na kallon haka a matsayin sata kai tsaye, inda suka yi kira da a kawo ƙarshe, amma kuma akwai waɗanda suke ganin cewa mutane ne da kawai suke kwasar abin da ya zama halaliyarsu.
Kana ana bayyana matakin da masu kwasar ganimar suka dauka a matsayin jarumi Robin Hood, wato karɓe abu daga hannun attajiri a kuma bai wa talaka.
Faye-fayen bidiyon sun nuna yadda masu wawason ganimar ke mika wa almajirai, tsofaffi, da masu nakasa da ba su da karfin shiga turmutsutsun.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Amma akasarin abin da aka fi bayyana wa sace-sacen da aka shaida, sakamakon 'yan dabar da suka yi kutse ne cikin zanga-zangar lumana kan nuna adawa da rundunar musammam ta SARS ne.











