Yadda aka yi kuskuren sanar da mutuwar mutum alhali da ransa

Wani Ba'indiye mai shekara 74 wanda aka yi kuskuren sanar da ya mutu kuma aka ajiye shi ɗakin ajiye gawa a jihar Tamil Nadu, ya mutu bayan ceto rayuwarsa.
A ranar Litinin aka sanar da cewa Mista Balasubramanyam ya mutu bayan kai shi asibiti. Ba a san me yake damunsa ba.
An ajiye shi a wurin ajiye gawa har kwana ɗaya kafin zuwan masu karɓar gawa da suka gano cewa bai mutu ba jikinsa yana rawa.
Nan take aka ɗauke shi zuwa wani asibiti amma kuma Allah Ya karɓi ransa a ranar juma'a
Shugaban asibitin ta gwamnati a kudancin birnin Salem, Dr Balajinathan, ya ce lokacin da aka kwantar da mutumin ba ya cikin hayyacinsa kuma ya rasu ne sakamakon matsalar da ta shafi numfashi.
Ya shaida wa sashen BBC na Tamil cewa ba a san adadin sa'o'in da Mista Balasubramanyam ya shafe a cikin na'urar ajiye gawa ba.
Bayan sanar da ya mutu a wata asibiti mai zaman kansa, iyalansa sun ɗauki gawarsa zuwa gida.
Sun kuma sanar da cewa za su binne shi ranar Talata.
Kamfanin da ke kula da binne gawa ya shaida wa ƴan uwan mamacin cewa "ya sanya hannu kan wata takarda kafin ya mutu."
Shugaban ƴan sandan yankin, Senthil Kumar ya ce iyalansa sun kasa bayar da takardar shaidar rasuwarsa.
Ƴan sandan sun shigar da bayanai da ke ƙalubalantar iyalan kan laifin sakaci da rayuwar ɗan Adam.
Mista Balasubramanyam yana da mata da ƴaƴansa mata biyu kuma yana zama tare da ɗan uwansa.
Ba a san yadda har ya rayu ba a cikin wurin ajiye gawa duk da tsananin sanyin da ke cikin akwatin - Haka kuma an kaddamar da bincike kan asibitin mai zaman kanta inda aka fara sanar da cewa ya mutu.
BBC ta yi ƙoƙarin tuntubar asibitin mai zaman kanta da kuma danginsa amma dukkaninsu ba su ce komi ba, kuma babu wani bayani daga likitan da ya sanar da cewa ya mutu.











