Coronavirus a duniya: Me ya kamata mata su yi game da aiki bayan kullen Covid-19?

Asalin hoton, Getty Images
Kamar sauran mata da suka yi nasara a wurin aikinsu, Simone Ramos na ganin cewa sai ta yi aiki tuƙuru sama da ko wane namiji kafin ta kai babban matsayi.
Ms Ramos wadda babbar manaja ce a wani kamfanin inshora ta bayyana cewa a matsayinta na shugaba kuma mace a kamfanin da maza ke da rinjaye, hakan ya tilasta mata take ƙara ƙaimi a wurin aiki a kullum.
"A farkon lokacin da na fara aiki, na yi tunanin cewa zan bar aikin nan gaba, Ina da buƙatar na ƙaro ilimi, Ina da buƙatar na nuna cewa na fi duk wani namiji ninki uku," in ji Ms Ramos a wata tattaunawa da BBC.
Ms Ramos ta kasance mai bayar da shawara ga ƙungiyar mata da ke aiki a kamfanonin inshora a Brazil kuma za ta wallafa littafi kan irin wannan lamari a watan Oktoba.
Tana yawan bayar da shawara ga mata masu tasowa kan cewa za su iya cin nasara a rayuwa idan suka "mayar da hankali tare da sa kai da ƙoƙarin cimma burinsu".
Amma kamar sauran masana, ta damu ƙwarai kan ƙara takura wa mata masu aiki da ake yi a lokacin wannan annobar - kuma ko wannan zai iya ƙara mayar musu da hannun agogo baya.
"Yin aiki iri biyu a lokaci ɗaya"

Asalin hoton, Getty Images
Lamarin ya fi ƙamari ne a gidajen da iyaye ke ƙoƙarin yin aiki daga gida, kuma a daidai lokacin ne suke ƙoƙarin taimaka wa 'ya'yansu karatu daga gida ko kuma 'yan uwansu.
Kamar yadda ƙungiyar ƙwadago ta duniya wato ILO ta bayyana, mata ne dai ke ɗaukar duk wani nauyi na watanni tara wanda ba tare da an biya su ba.
"Ba wai a ɓoye yake ba cewa mata ne ke ɗaukar duk wani nauyi na lura da yara da yin ayyukan gida a gidaje da dama," in ji Justine Roberts, shugabar shafin intanet na Mumsnet, wanda shi ne shafi mafi girma da ke bayar da shawarwari ga iyaye a Birtaniya.
Ms Roberts ta bayyana cewa irin haka ne ke saka wa kullum ake hura wa mata wuta a ƙarshe sai a bar su cikin damuwa da wahala.
"Iyaye mata na damuwa kan cewa suna fuskantar barazanar kora, ko kuma samun matsaloli a wuraren aiki sakamakon sun kasa taɓuka wani abin kirki a wurin aiki kamar yadda suka saba," in ji Ms Roberts.
"Ko da matan suna ganin cewa aikin da suke yi ba su samun wata matsala, da dama na ganin cewa ba za su iya ɗorewa kan haka ba na tsawon lokaci."

Asalin hoton, Press handout
A cewarta, "akasarin mata na ƙoƙarin yin aiki iri biyu a lokaci ɗaya" - wasu kuma damuwa da matsalar kwakwalwa na saka su su rinƙa ji kamar za su bar aikin, ko kuma ma barin aikin a irin wannan lokaci na annoba.
Babu wani ci gaba a wurin aiki
"Ya kamata mu tsaya mu duba halin da mata suke ciki da kuma abubuwan da suke fuskanta a wuraren aiki," in ji Allyson Zimmermann, darakta a wata ƙungiya mai zaman kanta ta Catalyst da ke taimaka wa mata su ci gaba a wuraren aiki.
Ƙungiyar Catalyst ta shafe shekaru tana bin diddiƙin waɗanda suka yi digiri na biyu har mutum 10,000 matra da maza daga manyan jami'o'i 26 a Asia da Canada da Turai da kuma Amurka.
A bincikensu, sun gano yadda rashin ayyuka da za su ba su damar sakewa ke da illa a garesu da zarar sun haihu.

Asalin hoton, Getty Images
Amma akwai wasu abubuwan son rai da suke a bayyane da ke janyo rashin ci gaba ga mata, ko da kuwa suna da ƙarewa ko suna da yara ko babu.
Misali, akasarin mata a binciken da Catalyst suka yi ya nuna cewa akwai yiwuwar su fara aiki a ƙaramin mataki bayan sun yi digirinsu na biyu. Kuma idan maza na aiki na sa'o'i fiye da mata, hakan na taimakonsu a wurin aiki amma ba ga mata ba.
Maza waɗanda ke da digiri na samun ƙarin albashi da zarar sun sauya wurin aiki, sai dai albashin mata na ƙaruwa ne kaɗai bayan sun nuna cewa suna da hazaƙa ga manajojinsu.
"Dole mata sai sun ƙara matsa ƙaimi wurin aiki amma maza ana musu ƙarin girma idan suna aikinsu," in ji Ms Zimmermann.
"Akwai wannan tunanin da ake yi kan cewa idan mata na yin irin abin da maza ke yi, za su wuce su. Gaskiya ba haka ba ne," a cewarta.
Matsin tattalin arziƙi na ƙara ba su wahala

Asalin hoton, Getty Images
Wani sabon bincike da aka yi a Amurka ya nuna cewa irin wannan tunanin na son rai zai iya tasowa lokacin da ake wahalar tattalin arziƙi.
Wani bincike da aka yi ya nuna cewa mata na ƙoƙarin neman manyan muƙamai a kamfanoni - manyan daraktocin kamfanoni na shan wuya a lokacin da kamfanoni ke cikin wani hali.
Bayan wani bincike da aka gudanar a kamfanoni 1,100 tsakanin 2003 zuwa 2015, binciken ya gano cewa masu son zuba hannun jari na yawan bayar da goyon baya ga daraktoci mata idan abubuwa na tafiya daidai.
Sai dai kuma idan aka samu matsala a kamfanin, akwai yiwuwar za su daina goyon bayan da suke yi ga matan.
Corinne Post, daga Jami'ar Lehigh da ke jihar Pennsylvania ta Amurka, ta shaida wa BBC cewa: “Yana da matukar wahala a samu wasu dalilai idan ba na son kai da ake nunawa kan jajircewar mata a wurin aiki, ko kuma shin suna aiki kamar yadda ya kamata.”











