Coronavirus a duniya: Yadda Covid-19 ta kassara talakawa ta kuma haɓaka arzikin ma'aikata

Lucimara da 'ya'yanta biyu

Asalin hoton, Lucimara Rodrigues

Bayanan hoto, Lucimara ta shafe wata biyu zaune gida babu aikin yi
    • Marubuci, Daga Pablo Uchoa
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa

Idan kana aiki daga gida a wannan lokaci na annoba, to babu mamaki kudaden da kake kashewa sun ragu, babu kudin mota ko cin abinci a waje.

A lokaci guda kuma, milyoyin ma'aikata sun rasa ko an tilasta musu tafiya hutun dole, an rasa ayyukan yi sannan kafar samun kudi ta toshe.

Annobar ta jefa duniya cikin yanayi na bambarakwai wanda masana tattalin arziki ke cewa ya sha bamban da yanayi da aka tsinci kai a baya, na koma bayan tattalin arziki. Ya haifar da "tazara tsakanin masu daidaikun kudade", a cewar Neil Shearing, wani babban jami'i tattalin arziki.

"Wani kaso na al'umma na rayuwa cikin matsi ko rashi yayin da wasu kuma barazana fada wa cikin rashi suke fuskanta, a wani bangare kuma an samu karuwar kudaden shiga a asusun ajiya," in ji shi

'Ajiyar ban mamaki'

Ofisoshi da bankuna na rufe a London galibi daga gida ake aiki

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Ofisoshi da bankuna na rufe a London galibi daga gida ake aiki

Rebecca O'Connor wata kwararriya ce kan harkar kudade a kamfanin inshorar Royal London, kuma ita ce ta samar da shafin koyar da tattali na Good With Money.

Ta shaida wa BBC cewa tattalin arzikin kowanne mutum ya sha bamban, ga wasu kuma samun damar ajiya abu ne mai wahala.

Sai dai kwararru kamarta sun samu riba wajen samun ragin kudaden kashewa.

Babu batun sayen fetur don tuka yara a mota a kai su makaranta, ko bin ababen hawa na haya a shafe sa'a biyu, don haka ta samu rarar adana dala 450 a kowanne wata.

Ta kuma bayyana yadda babu ita babu batun sayen shayi ko abinci a wurin aiki, ko cefanen tafiya gida don haka ta sake samun rarar dala 100 a kowanne wata.

Haka kuma ta sake samun damar takaita kashe kudi a fannin yawon karshen mako da fita sayayya da iyali.

Zahirin abin da ke faruwa a dokar kulle

Masu aiki daga gida sun fi samun rarar ajiyar kudi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Masu aiki daga gida sun fi samun rarar ajiyar kudi

Sai dai ga kowanne mutum akwai yadda abubuwa suka kasance masa. Wasu da suka tsinci kansu cikin kangin kulle a Birtaniya sun ce za su kashe kudaden da suka tara wajen cimma burinsa na rayuwa, kamar kasaitaccen biki ko tafiya hutu mai tsayi a karade Asiya.

Masana a London sun yi sharhi cewa iyali daya ciki uku a London kudaden ajiyarsu sun karu, yayin da kashi daya cikin 5 ke cewa sun ragu sosai.

Ga iyalin da ke samun mafi kankantar kudin shiga, a wani bangare kashi 10 ciki 100 na kudaden ajiyarsu sun karu, idan aka kwatanta da kashi 29 cikin 100 na wadanda ke cewa ce sun yi kasa.

Ga wadanda ke aiki daga gida akwai yiwuwar albashinsu ya karu, don haka sun samu damar kara kudaden ajiyarsu.

A wani bangaren kuma, kashi 20 cikin 100 na iyalai sun ce kudaden rancen da suke karba ya karu a lokacin annobar, domin da dama sun dogara kan kudaden rance.

A customer poses for a photo near mannequins placed on the adjacent tables according to social distancing rules at the Varuna Gezgin cafe in Istanbul, Turkey, 02 June 2020.

Asalin hoton, EPA

Sai dai O'Connor ta ce wannan a wani bangaren bai hana wasu mutane kashe kudi ba, yayinda tatalin arzikin duniya har yanzu ke cikin yanayi na kila-wa-kala.

''Ina ga hanyar da tafi dace wa ita ce zuba kudaden a fanin da za a ga alfanunsu ko samun biyan bukatu a lokacin da ake iya fadawa cikin matsi,'' a cewarta.

''Abu mai muhimmanci shi ne mutum ya zauna cikin shiri, saboda idan ba a yi takatsantsan ba, ko tsara yanayin kashe kudi, kudade na salwancewa.''

Tasirin tattalin arziki

People queuing to collect unemployment benefits in Santiago, Chile, May 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Dokar kulle tayi tasiri ga ayyukan ma'aikata da dama

''Yanayin da tattalin arziki ya fada akwai bambanci, saboda tasirin hakan ba boyaye ba ne a fanin ma'aikata,'' kamar yadda Steven Kapsos, wani mai bincike a kungiyar kwadago ta duniya ya shaidawa BBC.

Yayin da tattalin arzikin masana'antu da kamfanoni da dama suka durkushe, akwai rukunin da wannan bai shafa ba. A cewar kungiyar kwadago, aiki kamar na sayar da kaya da masana'anatu da gine-gine da abinci ko otel-otel da yawon bude ido su ne wadanda dokar kulle ta yi wa lahani.

''Ma'aikata a wannan bangare da sauran wasu bangarorin ba su samu damar aiwatar da ayukansu kamar yadda suka saba ba saboda matakan dokar kulle,'' a cewar Kapsos.

Rashin lokutan aiki sun karu kan sama da miliyan 300 da ake da su a cewar hukumar kwadago ta duniya. Kuma wannan yanayi yafi yawa a yankunan Amurka da tsakiya Asiya da kashi 13 cikin 100 a kowanne nahiya sai kuma kasahen da ke da matsakaicin kudin shiga.

Mutane biliyan 1 da miliyan 6 ne wannan yanayi ya shafa - kusan rabin al'ummar duniya da suka kai matakin aiki kenan.

'Yanayi na mamaki'

Lucimara da 'ya'yanta biyu

Asalin hoton, Lucimara Rodrigues

Bayanan hoto, Lucimara ta shafe wata biyu zaune gida babu aikin yi

Lucimara Rodrigues ta na daya daga cikinsu. Matar mai shekara 35 'yar Brazil na aikin goge-goge a yankin Boston, shekarunta 16 da komawa Amurka.

Rodrigues ta shaidawa BBC cewa ta na samun $3,500 zuwa $4,000 a kowane wata tana aiki ne a gida magidanta masu hali - amma dokar kulle ya hana ta fita aiki.

''Mu [masu aikin gida] mun fada cikin yanayi na mamaki,'' a cewarta. ''Ban taba tsintar kai na cikin yanayi da zai zame mun tilas na zauna gida ba, ba tare da wani aiki ba kusan wata biyu.''

Mijin Rodriguez magini ne wanda shi ma aikinsa ya tsaya saboda annoba. Ma'auratan na da yara biyu, mai shekara 6 da 14.

Ta ce akwai wasu cikin wayanda take yiwa aiki da ke mata ''kirki'' sannan sun ci gaba da biyanta, duk da cewa ba za ta iya zuwa ta yi musu aikin ba.

Iyalan sun rage yawan siyayar da suke yi, sun kuma rage kona man fetur amma duk da haka kudaden da take iya tarawa babu yawa.

'Ko wa tasa ta fisshe shi'

A construction worker in the informal sector who has lost his job in South Africa

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ma'aikata biliyan 1.6 ke fuskantar barazanar rasa aiki a duniya

Ma'aikatan gida a Amurka - akasari bakar fata da bakin-haure - misalai ne na ma'aikata da sai dai ''kowa ya ceci kansa'' a lokacin annoba, a cewar Haeyoung Yoon, babban darakta a kungiyar ma'aikatan gida ta kasa.

Kungiyar ta yi hubbasa wajen samar da kudin tallafi na $400 ga ma'aikata dubu 10 da wannan annoba ta yi tasiri ga rayuwarsu.

Ma'aikatan gida ba sa samun wasu kudade na alawus-alawus ko kudi hutu, ko hutun rashin lafiya ko inshora ga lafiyarsu.

Wani bincike ya nuna cewa kashi 70 cikin 100 na ma'aikatan gida bakar fata sun rasa ayyukansu ko an rage musu albashi saboda dokar kulle.

Karuwar nuna wariya

A mother and her son eat at an open-air restaurant that is distributing food for families affected by the economic crisis in Belo Horizonte, Brazil, June 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bankin duniya da IMF sun yi gargadi kan Covid-19

Babban bankin duniya ya ce annobar korona za ta iya jefa mutum miliyan 100 cikin kangin talauci.

Shi ma asusun lamuni na IMF ya bukaci a samar da tsare-tsare da za su kau da bambanci da ake da su a wannan lokaci na farfadowa daga tasirin annobar ga tattalin arzikin duniya.

Gwamnatoci sun kashe $10tn a matakan karfafa tattalin arziki, sai dai IMF ya ce akwai bukatar sake zage damtse domin kare matalauta, da kuma samar da tallafin abinci da kudade.