Annoba a duniya: Annobar da dabbobi suka yaɗa wa mutane a tarihi

Swine flu pandemic come for Pig

Asalin hoton, Reuters

    • Marubuci, Daga Olaronke Alo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist, BBC Pidgin, Lagos
  • An wallafa

An gano wata sabuwar cuta bayan annobar korona a China, masana kimiyya sun bayyana cewa cutar ta samo asali ne daga aladu kuma za ta iya shiga jikin dan adam.

Masana kimiyya sun damu matuka inda suka ce nan gaba cutar za ta iya yaduwa tsakanin mutane da kuma yaduwa a fadin duniya.

Tuni kasashen duniya suka fara damuwa kan cewa ka da wannan cuta ta zama wata sabuwar barazana ga bil adama kamar yadda wasu cututtuka da suka faro daga dabbobi suka zama barazana kuma suka zama annoba ga duniya.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

Ga wasu daga cikin cututtuka da suka samo asali daga dabbobi kuma suka girgiza duniya.

Coronavirus dey linked to bats

Asalin hoton, Getty Images

Jemagu- Coronavirus /Sars

Covid-19 cuta ce mai yaduwa wadda ƙwayar cutar coronavirus ke haddasawa.

Ana tunanin cutar ta fara yaduwa tsakanin dan adam bayan mutane sun fara amfani da mayaccen jemage wurin hada maganin gargajiya a China.

Mutanen da suka fara kamuwa da cutar bincike ya nuna cewa sun ziyarci kasuwar siyar da naman ruwa ta Wuha a China, kuma masana kimiyya sun cimma matsaya kan cewa cutar ta samo asali ne daga halittu.

Tun bayan barkewar cutar a Disambar 2019, cutar ta kama sama da mutum miliyan 10 a duniya, sama da mutum 500,000 kuma sun mutu sakamakon cutar.

Har yanzu babu wani takamaiman magani ko kuma riga-kafi na cutar.

Bincike ya nuna cewa Jemagu ne suka jawo cututtuka da dama da suka yadu tsakanin mutane.

Misali, akwai cutar Hendra wadda ake samu akasari a Australia, da kuma cutar Di Nipah a Bangladesh da Malasiya inda cutar ta sami asali ne tun 1998, akwai kuma cutar numfashi ta Sars wadda ta barke a nahiyar Asia a 2002.

Mosquito

Asalin hoton, Getty Images

Sauro- Malaria

Cutar Malaria cuta ce da ke barazana ga bil adama, ana daukar cutar ne bayan macen sauro mai dauke da kwayar cutar ta ciji mutum.

A 2018, kusan rabin mutanen duniya na karkashin barazanar cutar Malaria.

Akasarin mace-macen da ake samu a sakamakon Malaria ana samun su ne a kasashen Afrika da ke yamma da Sahara.Amma duk da haka, wadanda ke yankin Kudancin Asia da kuma Gabashin Mediterranean da kuma Yammacin Pacific da Amurka na cikin barazanar kamuwa da wannan cuta.

A 2018, hukumar WHO ta bada rahoton cewa kusan mutum miliyan 228 na dauke da Malaria kuma mutun 405,000 ne suka mutu sakamakon cutar a shekarar.

Fruit bat pictured for 2010 at di Amneville zoo for France.

Asalin hoton, Getty Images

Jemagu- Ebola

Cutar Ebola, cuta ce da ke barkewa lokaci bayan lokaci akasari a kasashen Afrika.

Sakamakon yanayin cutar, masana kimiyya na da yakinin cewa ana samun cutar ne daga jemage, a wani lokaci kuma daga birai.

An fara gano cutar ne a 1976 kusa da Kogin Ebola a Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo.

Tun bayan nan, an ta samun barkewar cutar lokaci bayan lokaci, kuma an samu bullar cutar matuka a kasashen Afrika.

Tun bayan bullar cutar a karon farko, Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewa cutar ta kama sama da mutum 31,095 kuma sama da mutum 12,950 suka mutu sakamakon cutar.

Cutar na da riga-kafi wadda ake kira rVSV-ZEBOV.

Rats dey cause Lassa Fever

Asalin hoton, Getty Images

Ɓera- Zazzabin Lassa

Zazzabin Lassa cuta ce mai kisa wadda cutar Lassa ke haifarwa.

Mutane na kamuwa da cutar ne bayan sun ci abinci wanda wani na'uin bera ya yi wa fitsari ko kashi a kai.

An gano cutar ne tun a shekarun 1950 kuma ba a gano me ke jawo cutar ba sai a 1969.

Zazzabin Lassa cuta ce wadda ta yi ƙaurin suna a kasashen Benin da Ghana da Guinea da Liberia da Mali da Sierra Leone da Togo da kuma Najeriya, za kuma a iya samun cutar a wasu kasashen yammacin Afrika.

Ana amfani da maganin ribavirin wurin magance zazzabin na Lassa.

Ana samun kusan mutun 100,000-300,000 da ke kamuwa da cutar a duk shekara kuma kusan mutun 5,000 cutar ke kashewa.

Monkey pox dey linked to monkeys

Asalin hoton, Getty Images

Ƙyandar birai

Wannan cuta ce da ke yaduwa daga dabbobi zuwa mutane.

A Afrika, an gano shaidar wannan cuta a dabbobi daban-daban kamar kurege, da beraye da birai.

An fara gano wannan cutar ne a jikin dan adam a 1970 a Jamhuriyyar Dimokraddiyar Congo, kasashe 11 na Afrika sun tabbatar da bullar wannan cuta.