Za a fara sayar da litar mai a kan naira 123 a Najeriya

Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

A Najeriya, kamfanin man kasar ya rage fashin litar man fetur daga naira 125 zuwa naira 123.

Kamfanin ya umarci gidajen mai da su fara sayar da mai a kan sabon farashin daga ranar Litinin 1 ga watan Yunin, 2020.

Hukumar da ke kayyade farashin mai ta Najeriya ce ta sanar da sabon farashin man, wanda ta ce daga yanzu farashin litar mai ba zai wuce tsakanin  naira 121 da kobo hamsin zuwa 123.50 ba.

Kakakin hukumar, Mista Apolos Kimchi, ya shaida wa BBC cewa an rage farashin ne sakamakon faduwar da ya yi a kasuwannin duniya.

Tuni dai wannan mataki ya yi wa wasu 'yan Najeriya dadi, inda a bangare guda kuma bai yiwa wasu dadi ba saboda suna ganin da zarar komai lafiya a kasashen duniya sakamakon cutar korona to in har farashin man ya tashi, to ko shakka ba bu haka zai tashi ma a Najeriya.

Wasu 'yan Najeriyar da BBC ta zanta da su sunce, duk da an rage farashin man suna ganin ba a abin burgewa ba ne, saboda farashin mai ne kawai aka rage a cikin muhimman kayayyakin bukatun yau da kullum.

Suka ce, " A bangaren kayan abinci da sauransu ba bu abin da ya sauya, don haka su rage farashin mai bai burgesu ba".

To sai dai kuma rage rage farashin a wajen wasu 'yan Najeriyar, ya yi musu dadi musamman masu ababan hawa da ke bukar man.

Karin bayani

A karshen watan Maris, 2020 ne, gwamnatin Najeriya ta sanar da sake rage farashin man fetur zuwa naira 123 da kwabo 50 a duk lita daga naira 125 da ta rage da farko.

Gwamnatin Najeriyar ta ce an rage farashin ne bisa la'akari da yadda farashin danyen mai ya fadi a kasuwannin duniya sakamakon cutar coronavirus.

Farashin danyen man fetur ya yi mummunar faduwar da bai taba yin irinta ba cikin shekaru da dama a kasuwannin duniya.

Barkewar cutar Coronavirus a duniya ya shafi yadda ake sayen man a kasuwar duniya.

Bugu da kari jayayya tsakanin Saudiyya da Rasha, yasa man fetur din ya yi kwantai.

Masana tattalin arziki na ganin ya zama dole kasashen da ke da man su rage yawan wanda suke fitarwa kasuwannin duniya da nufin daga farashinsa.