Ba za mu rage farashin mai ba — IPMAN

Tanker mai

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Reshen jihar Kano na kungiyar manyan dillalan man fetur na kasa wato IPMAN, ya ce ba zai sayar da man fetur din da yake da shi a yanzu, a kan sabon farashin da gwamnati ta bayar ba.

Shugaban kungiyar reshen jihar Kano, Bashir Dan Mallam, ya shaida wa BBC cewa ko shakka babu sun yi farin ciki da sanarwar gwamnatin a kan rage farashin man.

Amma kuma suna masu tabbatar da cewa sai man da suke da shi a yanzu ya kare tas, kafin su koma sayar da mai a kan sabon farashin gwamnati na naira 123.50k.

Ya ce " Ba wai zamu bijirewa umarnin gwamnati ba ne, mu 'yan kasa na gari ne masu bin doka, amma kuma mun dauki wannan mataki ne bisa la'akari da irin asarar da muka tabka a baya lokacin da aka sanar da cewa farashin mai ya koma naira 125 kan kowacce lita".

Bashir Dan Mallam, ya ce " Da muka tattara alkaluman irin asarar da muka yi mun ga cewa mun yi asarar fiye da naira biliyan biyar, don haka a wannan lokacin sam ba za muyi ba".

Ya ce idan aka cire gwamnatin tarayyar wajen daukar yawan ma'aikata, babu wanda ya kai su yawan ma'aikata.

Bashir Dan Mallam, ya ce dalilinsu na biyu kuma na daukar wannan mataki shi ne, ya kamata ace an tuntubesu a matsayinsu na wadanda suke harkar mai, don aji ra'ayinsu amma ba ayi hakan ba.

Shugaban kungiyar na Kano, ya ce " To bisa wadannan dalilai namu, mun tuntubi masu ruwa da tsaki kan wannan harka da ma kamfanin man na kasa NNPC, mun kuma kai kokenmu sannan sun fahimcemu, an bamu dama tsoffin kayanmu su kare, sannan mu koma sayar da man a kan sabon farashin na naira 123.50k.

Ya ce "Dukan ne ya mana yawa, amma da zarar man da muke da shi ya kare, mun kawo sabo, to zamu koma sayar da man a kan sabon farashin gwamnatin".

Bashir Dan Mallam, ya ce " Da yawa daga cikinmu sun samu matsala saboda rage farashin man da aka yi a baya, don haka muka yanke shawara cewa a wannan karon ba zamu bari mu maimaita abin da ya faru damu a baya ba".

Karin bayani

A karshen watan Maris, 2020 ne, gwamnatin Najeriya ta sanar da sake rage farashin man fetur zuwa naira 123 da kwabo 50 a duk lita daga naira 125 da ta rage da farko.

Gwamnatin Najeriyar ta ce an rage farashin ne bisa la'akari da yadda farashin danyen mai ya fadi a kasuwannin duniya sakamakon cutar coronavirus.

Farashin danyen man fetur ya yi mummunar faduwar da bai taba yin irinta ba cikin shekaru da dama a kasuwannin duniya.

Barkewar cutar Coronavirus a duniya ya shafi yadda ake sayen man a kasuwar duniya.

Bugu da kari jayayya tsakanin Saudiyya da Rasha, yasa man fetur din ya yi kwantai.

Masana tattalin arziki na ganin ya zama dole kasashen da ke da man su rage yawan wanda suke fitarwa kasuwannin duniya da nufin daga farashinsa.

Karin bayani kan coronavirus