Ana samun mace-macen dabbobi a Najeriya

Dabbobi

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

A yayin da ake ta samun rahotannin mace-macen mutane a sassa daban-daban na arewacin Najeriya, wasu makiyaya sun ce su ma dabbobi na mutuwa barkatai a halin yanzu a wasu sassan yankin.

Shugaban kungiyar matasa makiyaya na shiyyar arewa maso gabashin Najeriyar, Abdurrahman Buba Kwacham, ya shaida wa BBC cewa, sai da suka gudanar da bincike sannan suka gano cewa a yanzu haka ana asarar dabbobi na fitar hankali.

Ya ce, dalili kuwa shi ne mutane sun kiwota dabbobi masu yawa na tsawon lokaci amma idan sun je kasuwa domin su siyar ba bu kasuwa, sannan kuma su masu dabbobin ba su da wadataccen abincin da zasu rinka ba wa dabbobin.

Abdurrahman Buba Kwacham, ya ce " Ba zan iya cewa ga adadin dabbobin da suka mutu ba musamman a jihohin Adamawa da Zamfara da Kano da Jigawa da Sokoto da Kebbi da kuma Kaduna, Allah ne kadai ya san adadinsu".

Ya ce akalla dabbobin da suka mutu za su kai dubu biyar zuwa dubu shida, wannan kuma babbar asarar ce ga masu kiwo wadanda ke kiwon don su samu abinci.

Abdurrahman Buba Kwacham, ya ce " Ba wata cutar ce ke kashe wadannan dabbobinba in banda yunwa, karancin abincin da dabbobin zasu ci shi ke hallaka su".

Ya ce wannan dokar kullen da aka sanya a kusan dukkan jihohin Najeriyar saboda yaduwar cutar korona, na da nasaba da yunwar da dabbobin suka tsinci kansu ciki.

Makiyayin ya ce, mutuwar dabbobin babbar asara ce ga mai su da kasa kai hatta tattalin arzikin kasar ma ya yi asarar saboda mace-macen dabbobin.

Ya ce " Mun sanar da likitocin dabbobi a kan mace-macen dabbobin inda suka tabbatar mana cewa yunwa ce ke kashesu ba wata cuta ba".

Abdurrahman Buba Kwacham, ya ce a yanzu sun rubuta wa gwamnati da hukumomin da wannan iftila'i ya shafa takarda don azo a dauki matakin da ya ce cikin gaggawa.

Ya ce," Muna kuma kira ga gwamnatin tarayya da ta jihohi da ma kananan hukumomi da su yi maza su kawo dauki a kan mace-macen dabbobin, domin dabbobi nau'ine na abinci".

Karin bayani kan coronavirus