Tun bayan barkewar annobar cutar korona al'amura da yawa suka sauya a duniya. Hakan na faruwa a kokarin dakile yaduwarta.
Wannan abu ya shafi yadda ake sallah a masallatai, yayin da wasu masallatan suka dakatar da sallar jam'i wasu kuwa sun ci gaba da yi amma fa da sabon salon buda sahu da rashin hada kafadu.
Ga wasu zababbun hotuna daga kasashe daban-daban na yadda ake yin sallar jam'i a yanzu.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Hoton da aka dauka a ranar 24 ga watan Afrilu, da ke nuna wasu mutane na sallah kusa da Ka'aba a filin Masallacin Makka, wurin da ya fi kowanne tsarki wajen Musulmai, a ranar farko ta watan da ya fi kowanne tsarki na Ramadana, yayin da ake tsaka da haramcin tarukan iyalai da ibada saboda cutar korona
Asalin hoton, Haramain Sharifain
Bayanan hoto, Wannan hoton shafin da ke kula da Masallatai Biyu Masu Daraja ne ya wallafa a shafin Facebook dinsa, kwana na biyu da fara azumi inda ake Sallar Asham
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wasu Falasdinawa da ke Sallar Tarawih a kofar Asbat wajen Aasallacin Aqsa cikin watan Ramadana a birnin Jerusalem a ranar 26 ga watan Afrilu 2020.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wasu Musulmai na sallah a Masallacin Jama da ke birinin Delhi na Indiya, a ranar Juma'a 25 ga watan Afrilun 2020, tare da ba da tazara tsakaninsu duk da cewa an rufe wurare da yawa na masallacin amma ana barin wasu kalilan su shiga.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wasu Falastinawa da Larabawan Isra'ila sun bar tazarar mita bibbiyu tsakaninsu saboda cutar korona, yayin da suke sallah kusa da wajen wani ajiye mota da ke birnin Tel Aviv na Isra'ila bayan shan ruwa, a rana ta biyu na Azumin Watan Ramadana mai tsarki ranar 25 ga watan Afrilun 2020.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Musulmai a kasar Nepal na gudanar da sallah a Masallacin Kashmeeree a ranar farko ta Azumin Ramadana yayin da ake fama da dokar hana fita saboda cutar korona. Musulmai a Nepal na gudanar da azumi yayin da ake fama da dokar kulle. Haka kuma gwamnatin kasar ta haramta manyan tarukan addinai.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Masu ba da agajin gaggawa a Pakistan da wasu mutane na wa wani abokin aikinsu sallar gawa daga nesa wanda ya mutu dalilin korona a ranar 25 da watan Afrilun 2020
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Imam Magdy Badr na jan Sallar Jam'i kai tsaye ta na'urarsa a Masallacin Al-Salaam da ke birnin Dearborn a Michiganda da kusan babu kowa. Saboda tabbatar da tazara tsakanin mutane ana yin sallar a warware a irin matakan da duniya ke dauka da kaucewa annobar cutar korona. An dauki hoton ne a ranar 24 ga watan Afrilun 2020.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Babban mai ba da fatawa na kasar Bosniya da Herzegovina Husein Kavazovic na gabatar da Sallar Juma'a ta farko a cikin Ramadana tare da wasu mutane kalilan yayin da ake tsaka da annobar korona a masallacin Gazi Husrev-beg a Sarajevo ranar 24 ga watan Afrilun 2020.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Musulmai a Indonesia na gabatar da Sallar Tarawih cikin Azumin Ramadan a Masallacin Jogokriya a yogyakarta a ranar 24 da watan Afrilu 2020. Musulmai na azumi daga fitowar rana zuwa faduwar rana