Coronavirus: Hotunan sabon salon Sallar Jam'i da annobar ta jawo

An wallafa

Tun bayan barkewar annobar cutar korona al'amura da yawa suka sauya a duniya. Hakan na faruwa a kokarin dakile yaduwarta.

Wannan abu ya shafi yadda ake sallah a masallatai, yayin da wasu masallatan suka dakatar da sallar jam'i wasu kuwa sun ci gaba da yi amma fa da sabon salon buda sahu da rashin hada kafadu.

Ga wasu zababbun hotuna daga kasashe daban-daban na yadda ake yin sallar jam'i a yanzu.