Ana zargin mai wa'azi da yada wa dubban mutane coronavirus

Asalin hoton, Getty images
Hukumomin jihar arewacin Indiya ta Punjab sun kebe mutane kimanin 40,000 a wasu kauyuka guda 20 bayan barkewar cutar Covid-19 wadda ake alakanta wa da wani mutum da ya kai cutar can.
Mutumin mai shekara 70 ya mutu sakamakon annobar koronabairus - lamarin da aka gano bayan mutuwarsa.
Mutumin wanda mai wa'azi ne, ya yi biris da shawarar ya killace kansa bayan ya koma gida daga wata tafiya zuwa kasar Italiya da Jamus kamar yadda jami'ai suka fada wa wakilin BBC a Punjab, Arvind Chhabra.
Indiya a yanzu na da mutum 640 da aka tabbatar sun kamu da kwayar cutar, cikinsu 30 'yan Punjab ne.
Sai dai, kwararru na bayyana damuwar cewa hakikanin adadin masu dauke da cutar na iya zarce haka da gasken gaske.

Asalin hoton, AFP
Indiya na da daya daga cikin kasashe masu karancin gwajin mutanen da ake zargi na da cutar koronabairus a duniya, ko da yake ana ta kokarin bunkasa wannan aiki.
Ana fargabar cewa barkewar annoba a kasa mai mutum biliyan 1 da miliyan 300 na iya zama wani babban bala'i.
Mutumin wanda aka bayyana sunansa Baldev Singh, ya ziyarci wani babban taro don shagalin bikin Hola Mohalla na mabiyan addinin Sikh kafin mutuwarsa.
Bikin na tsawon kwana shida na jan hankulan kimanin mutum 10,000 a kullum.

Asalin hoton, AFP
Sai dai mako guda bayan mutuwarsa, gwajin da aka yi wa danginsa ya tabbatar da cewa mutum 19 sun kamu da koronabairus.
Wani babban jami'i ya fada cewa "Zuwa yanzu, mun iya bin sawun 550 cikin mutanen da suka yi hulda da shi kai tsaye amma adadin yana karuwa. Mun killace kauye 15 a yankin da ya je ziyara".
An sake rufe wasu kauyuka guda biyar da ke kusa da lardin da abin ya faru.
Ba dai wannan ne karon farko da cudanya da wani mai cuta ya janyo kebe dumbin mutane ba a Indiya.
A Bhilwara, wani birni mai masakun atamfa da ke jihar Rajistan ta arewacin Indiya, ana fargabar cewa wani ayarin likitoci da wani maras lafiya ya harba wa cutar, mai yiwuwa ne sun yada ta ga daruruwan mutane.
An sanya matakin hana fita ga mutum 7,000 da ke kauyuka masu makwabtaka da birnin.
Gwamnatin Indiya ta ayyana rufe kasar ba shiga ba fita na tsawon kwana 21, ko da yake ba a hana mutane su fita don sayen kayan abinci da magunguna ba.










