Ciwon koda: Mu 10 muka rayu cikin mutum 160 a Najeriya
Yayin da aka gudanar da bikin ranar koda a fadin duniya don wayar da kan jama'a game da illon da ke tatattare da ciwon, wani mai fama da ciwon koda kuma Shugaban masu fama da ciwon a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Malam Wali Ado Rano ya ce masu fama da wannan larura na fuskantar kalubale da dama.
Malam Wali Ado Rano ya fada wa BBC hakan ranar bikin koda ta duniya da ake gudanarwa ranar 12 ga watan Maris din kowace shekara.
Ya ce sai da aka yi masa wankin koda na tsawon shekara guda kuma hakan ba wai yana nufin mutum ya samu lafiya ba ne saboda mara lafiyar zai ci gaba da shan magunguna ne har tsawon rayuwarsa.
"Da farko ana yi min wankin koda sau daya a sati, aka koma sau biyu sai da aka kai kuma sau uku, a lokacin ana yi min wankin koda sau daya akan naira dubu 14," in ji shi.
Ya kuma bayyana halin da mara lafiya ke shiga idan za a yi masa wankin kodar "lokacin da ake cikin yin wankin kodar, jinin mutum na daukewa sannan akwai allura naira dubu shida zuwa dubu takwas,"
Malam Wali Ado Rano ya ce ya kashe sama da naira miliyan 15 domin a yi masa dashen koda a India kuma "ba ni da wata matsala sai ta sayen magani kuma maganin babu shi a Najeriya."
"A wata ina shan maganin kimanin naira dubu dari da hamsin." a cewarsa.
Matsalar da masu ciwon ke fuskanta
Malam Wali Ado Rano ya ce "wadanda muka rika yin wankin koda kusan mu 160 a lokacin, kusan ba mu fi mu 10 ba wadanda muka rayu, wadanda bas u samu an je an yi musu dashen kodar ba.''
Ya bayyana cewa ciwon koda harka ce ta kudi saboda "wannan wankin kodar ya zama wajibi idan har mutum na son ya ci gaba da rayuwa, rayuwa ce ba a cikin dadi ba."
Sai dai Malam Ado Rano ya roki gwamnatin Najeriya ta inganta asibitocin kasar tare da mayar da wankin kodar ya zama a kyauta domin sawwake wa mara lafiya.
A cewarsa, "an yi wani bincike wadanda manyan masana suka yi a Hadeja, ya kamata a fito da sakamakon binciken a gano dalilin da yasa mutane suke fama da ciwon, ciwo ne da a yanzu babu tsoho babu yaro babu mace babu namiji."












