Indiya: An harbi mawakiya a fuska don ta dakata da casu

The woman was shot in the face at a wedding celebration

Asalin hoton, Susheel Shukla

Bayanan hoto, An harbi matar ne a fuskarta a lokacin da ta dakata da yin rawa a wajen biki
An wallafa

An kwantar da wata mawakiya a asibiti bayan da aka harbe ta a fuska saboda ta dakatar da wani casu da take tsaka da yi a wajen liyafar biki.

A wani bidiyo da ke nuna yadda abin ya faru, an nuna matar na rawa a kan dandamali. Sai ta dakata, sannan ta fadi tana tallabe da fuskarta.

'Yan sanda sun shaida wa BBC cewa sun gano wanda ya harbeta din a cikin bidiyon, kuma tuni ya tsere.

Lamarin ya faru ne a yayin wata liyafa da aka yi ranar 1 ga watan Disamba a wani kauye da ke jihar Uttar Pradesh.

Sai dai abin bai bayyana ba sai bayan kwanaki, bayan da bidiyon ya yadu a kafafen sada zumunta.

'Yan sandan sun shaida wa BBC cewa: "Mutumin ya tsere amma muna da tabbacin cewa za mu kama shi nan ba da jimawa ba."

Rikici a lokacin biki ba bakon abu ba ne a wasu sassan kasar, inda mahalarta kan je da bindigogi - wadanda mafi yawanci kan yi hakan ne don harbi a iska domin nuna farin ciki.

Wani lamarin irin wannan ya faru a shekarar 2016 a jihar Punjab da ke kudancin kasar, inda aka kashe wata mai ciki bayan da aka harbe ta a cikinta lokacin da take rawa a wajen biki.

Wasu lamarun irin haka da suka fari.

A watan Nuwamban 2016 wata mata dauke da bindiga da ta yi ikirarin ita abar bauta ce ta kashe mutum uku ciki har da goggon angon, bayan da ta harba bindigar taya murna a jihar Haryana.

A shekarar 2018, 'yan sanda a Punjab sun kama wani mutum bayan zarginsa da harbe makwabciyarsa bisa kuskure a lokacin wata liyafar aure.

Ya yi harbi a iska har sau a iska don nuna farin cikin auren 'yarsa da za a yi. Amma daya daga cikin harsasan suka sami makwabciyarsa a goshinta kuma ta mutu nan take.