An kona matar da za ta je kotu kan shari'ar fyade a Indiya

Masu zanga-zanga rike da allon da aka rubuta a kawo karshen dabi'ar yi wa mata fyade, a lokacin da wasu gungun maza suka yi wa mace 'yar shekara 27 fyade a Hyderabad

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shekaru da dama kenan da ake nuna damuwa kan cin zarafin mata ta hanyar lalata da su a kasar Indiya
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Matar mai shekara 23 da akai zargin an yi wa fyade, tana gadon asibiti cikin mawuyacin hali bayan an banka mata wuta a lokacin da take shirin tafiya kotu a Indiya.

Tun a watan Maris ne matar ta shigar da karar wasu maza biyu, kuma ta na kan hanyar zuwa kotu don fara sauraren karar a jihar Uttar Pradesh.

Tana cikin mawuyacin hali a gadon asibiti, kusan dukkan jikinta ya kone.

'Yan sanda sun ce sun kama maza biyar da ake zargi da banka mata wutar, ciki har da wadanda ake zargi da yi mata fyade.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru a lokacin da take hanyar zuwa tashar jirgin kasa, a daidai lokacin ne gungun mazan suka far mata tare da jan ta zuwa wani fili da ke kusa da wurin, nan take suka cinna mata wuta.

Gundumar Unnao da abin ya faru ta yi kaurin suna wadda a baya-bayan nan, ta karade kafafen yada labarai sakamakon wani zargin yin fyade ga wata yarinya karama.

A watan Yuni ne 'yan sanda suka fara binciken kisan kai, ga dan majalisar da ke wakiltar yankin bayan matar da ta zargi ya yi mata fyade da yin mummunan hadarin mota.

Daga bisani kuma aka kashe biyu daga cikin gwaggwanninta, tare da ji wa lauyanta mummunan rauni.

Lamarin na baya-bayan nan ya janyo zazzafar zanga-zanga a daukacin kasar Indiya, wadda har yanzu take cikin kaduwar aikata kisan da fyade da kuma shi ne babban labari a kafafen yada labarai.

A ranar 27 ga watan Nuwamba aka yi wa wata 'yar shekara 27 fyade aka kuma nemeta aka rasa, sai daga bisani aka gano gawar ta a kone mako guda bayan batanta a kudancin birnin Hyderabad.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Presentational white space
Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Presentational white space
Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Presentational white space

Batun cin zarafin mata da yi musu fyade a Indiya na ci gaba da daukar hankali tun daga watan Disambar shekarar 2012.

Mafi tashin hankali a ciki shi ne wanda aka samu gungun maza da yi wa wata karamar yarinya fyade a motar bas tare da hallakata a birnin Delhi.

Samun raguwar cin zarafin matan a Indiya, duk kuwa da ikirarin hukumomi na daukar matakan gurfanar da wadanda ake zargi gaban shari'a.

Kididdigar gwamnati kan aikata kuggan laifuka ta baya-bayan nan, ta nuna cewa 'yan sanda sun yi rijistar zargin aikata fyade sau 33,658 a kasar Indiya a shekarar 2017, wato kenan ana samun a kalla mata 92 da aka yi wa fyade a kowacce rana.

Presentational grey line