Jonathan ya ziyarci Buhari

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wata ganawa da magabacinsa, Goodluck Jonathan a fadar gwamnati da ke Abuja.

Shugaba Muhammad Buhari na Najeriya na maraba da tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan.

Asalin hoton, TWITTER/GARBA SHEHU

Bayanan hoto, A ranar Alhamis tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ziyarci shugaba Buhari

Kakakin shugaban kasar, Garba Shehu ya sanar da haka a shafinsa na tuwita cewa shugaban ya karbi bakuncin Jonathan a fadar gwamnati, sai dai bai fayyace dalilin ganawar ba.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Jonathan ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari a fadar gwamnati ne a ranar Alhamis inda aka ga shugabannin biyu cikin sakin fuska da walwala.

Ganawar da Shugaba Buhari ya da Jonathan a fadar gwamnati

Asalin hoton, TWITTER/GARBA SHEHU

Bayanan hoto, Shugaba Buhari ya karbi bakuncin tsohon shugaban Goodluk Jonathan a fadar gwamnati

Jonathan ya sauka daga mulkin kasar ne a ranar 29 ga watan Mayun 2015, bayan da Buhari ya kayar da shi a babban zaben kasar. Daga nan ne shugaba Buhari ya fara wa'adin mulkinsa na farko a matsayin farar hula a karkashin jam'iyyar APC.

Ganawar da Shugaba Buhari ya da Jonathan a fadar gwamnati

Asalin hoton, TWITTER/GARBA SHEHU

Bayanan hoto, Shugaba Buhari ya karbi bakuncin tsohon shugaban Goodluk Jonathan a fadar gwamnati

Ana ganin abin da tsohon shugaban ya yi a lokacin, inda ya kira Buhari ta waya kuma ya taya shi murnan cin zabe tun kafin hukumar zaben kasar ta sanar da sakamakon a matsayin wanda ya fara kafa irin wannan tarihi a siyasar nahiyar Afirka.