Jonathan ya ziyarci Buhari

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wata ganawa da magabacinsa, Goodluck Jonathan a fadar gwamnati da ke Abuja.

Kakakin shugaban kasar, Garba Shehu ya sanar da haka a shafinsa na tuwita cewa shugaban ya karbi bakuncin Jonathan a fadar gwamnati, sai dai bai fayyace dalilin ganawar ba.

Jonathan ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari a fadar gwamnati ne a ranar Alhamis inda aka ga shugabannin biyu cikin sakin fuska da walwala.

Jonathan ya sauka daga mulkin kasar ne a ranar 29 ga watan Mayun 2015, bayan da Buhari ya kayar da shi a babban zaben kasar. Daga nan ne shugaba Buhari ya fara wa'adin mulkinsa na farko a matsayin farar hula a karkashin jam'iyyar APC.

Ana ganin abin da tsohon shugaban ya yi a lokacin, inda ya kira Buhari ta waya kuma ya taya shi murnan cin zabe tun kafin hukumar zaben kasar ta sanar da sakamakon a matsayin wanda ya fara kafa irin wannan tarihi a siyasar nahiyar Afirka.