An sace tokar gawar Mahatma Gandhi

Asalin hoton, Getty Images
Barayi sun sace wani bangare na tokar gawar Mahatma Gandhi a daidai lokacin da ake murnar cikarsa shekara 150 da haihuwa, in ji 'yan sanda a kasar Indiya.
An dauke tokar ne a wani ginin tuna wa da tsohon gwarzon a yankin tsakiyar Indiya, inda ake ajiye da shi tun 1948 - shekarar da aka kashe Ghandi, mai tsattsauran ra'ayin Hindu.
Barayin sun rubuta "maci amana" da koren fenti a kan hotunansa.
Wasu mabiya addinin Hindu na ganin Gandhi a matsayin maci amana bisa tsarinsa na hadin kan addinan Hindu da Musulunci duk da cewa rikakken dan Hindu ne.
'Yan sanda a Rewa, a jihar Madhya Pradesh sun shaida wa BBC cewa suna binciken satar.
Mangaldeep Tiwari, mai kula da inda tokar take ajiye ya ce satar abin kunya ce.
"Na bude kofar ginin Bhawan da sassafe saboda bikin zagayowar ranar haihuwar Ghandi ce," ya shaida wa shafin The Wire na kasar indiya.
"Da na dawo wajen karfe 11:00, na samu an sace tokar kuma na lalata hotonsa."
'Yan sanda sun dauki mataki bayan da Gurmeet Singh, shugaban jam'iyyar Congress na yankin ya kai korafi.
"Dole ne a daina wannan rashin hankalin," in ji Mista Singh.
"Ina kira ga 'yan sandan Rewa da su duba na'urar daukar hoto ta CCTV da ke cikin Bapu Bhawan."


Ghandi ya jagoranci fafutuka ta lumana don kwato Indiya daga mulkin mallakar Burtaniya, inda ya zama gwarzo ga dumbin mutane a fadin duniya.
Indiyawa da yawa na kallonsa a matsayin "Uban Kasa".
Wani mai tsananin kishin addinin Hindu ya kashe shi a shekarar 1948.
Bayan mutuwarsa, an kona gawarsa, amma ba a watsa tokar a kogi ba kamar yadda addinin Hindu ya tanada.
Saboda shahararsa, an debi wani bangare na tokar gawar an aika da shi wasu wuraren ajiyar kayan tarihi- ciki har da na Bapu Bhawan.











