Ruwa ya yi barna a biranen India

Ambaliyar ruwa a India

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu aikin ceto na amfani da kwale-kwalen roba dan isa wasu yankunan kasar
An wallafa

Sama da mutane 100 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a arewacin India sakamakon tunbatsar da kogin Ganga ya yi.

An sheka ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihohin Bihar da Uttar Pradesh, ya yin da masu aikin ceto sukai nasarar kwashe dubban mazauna yankin.

Ambaliyar ruwan ta daidaita birnin Patna mai mutane miliyan biyan biyu. Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwa ya kusa shafe motoci.

Tashoshin jirgin kasa, da mota, da asibitoci da makarantu duk ambaliyar ta shafa. Ya yin da aka samu katsewar wutar lantarki a Patna da Uttar Pradesh.

Haka kuma ruwan ya shafi gidan Kurkuku, lamarin da ya sanya dole hukumomi suka kwashe sama da fursunoni 500 daga gundumar Ballia sakamakon shanye gine-gine uku da ruwan ya yi.

A baya dai ruwa na janyewa a watan Satumba a kasar India, amma yanzu masu hasashen yanayi sun damunar ba na ta musamman ce da aka dade ba a gani ba cikin shekaru 50.

Asibitin Uttar Pradesh
Bayanan hoto, Ruwan ya shiga wasu asibitoci da ke Uttar Pradesh
Ruwa ya shanye tituna da hanyoyin sufuri
Bayanan hoto, Jami'an lafiya na dauke da mara lafiya a cikin ruwan
Ruwa ya shanye tituna da hanyoyin sufuri
Bayanan hoto, Jami'an lafiya na dauke da mara lafiya a cikin ruwan
Ambaliyar ruwa
Bayanan hoto, Damunar bana ta zo da mamakon ruwan da aka dade ba a gani a India