Firaministan India ya ce kasar ta kawo karshen yin bahaya a fili a kauyuka

Wani yaro na bahaya a gefen titin dogo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Miliyoyin 'yan kasar India na kashi a fili, saboda ba su bandaki
An wallafa

Firaministan India Narendra Modi ya ayyana cewa daga yanzu an kawo karshen al'adar nan ta yin bahaya a fili a yankunan karkara na kasar, sakamakon shirin da gwamnati ta bullo da shi na gina miliyoyin ban-daki.

Mista Modi ya bayyana hakan ne a lokacin bikin cika shekara 150 na zagayowar ranar haihuwar Mahatma Gandhi, wanda akidunsa suka zamo jigo ga yakin neman zaben Firaministan.

Jim kadan bayan da ya dare kujerar mulkin kasar ne, Narendra Modi ya kaddamar da shirinsa mai cike da buri na tsaftace India.

Wani bandaki na jama'a da gwamnati da yi a kusa da kauyen Bihar, a arewacin India

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani bandaki na jama'a da gwamnati da yi a kusa da kauyen Bihar, a arewacin India

Tsafta tana daga cikin wani muhimmin bangare na burinsa na ganin ya bunkasa Indiaa ta zama babbar kasa ta zamani mai karfi.

A bisa wannan akida da manufa tun daga wannan lokaci zuwa yanzu an gina miliyoyin ban-daki a kasar musamman ma a yankuna na karkara inda ake da al'adar yin kashi a fili.

Kuma yawan 'yan karkara da suke da hanyar samun bandaki mai kyau da tsafta wanda ya dace ya karu sosai.

Narendra Modi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yana daga cikin babban burin Firaminista Narendra Modi ya kawo karshen al'adar yin bahaya a fili a India

Da kaiwa wannan matsayi jihohin kasar na fuskantar matsin lamba na siyasa kan su ayyana cewa ba su da sauran matsalar yin bahaya a fili a yanzu, wato dai al'adar ta zama sai tarihi.

To amma gudun kada a yi riga-mallam-masallaci, ya sa wasu ke ganin cewa ya yi wuri a yi wannan sanarwa domin akwai bandakuna da yawa da ba a kammala aikinsu, ko ba sa aiki ko kuma ba a ma amafani da su ba.

Gwamnatin India ta samar da bandakuna da dama a yankuna na karkara don magance matsalar yin bahaya a fili

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gwamnatin India ta samar da bandakuna da dama a yankuna na karkara don magance matsalar yin bahaya a fili

Saboda haka akwai sauran lokaci da kasar ta India za ta fito ta bayyana cewa ta ga bayan matsalar yin bahaya a fili.

Miliyoyin 'yan India na kashi a fili saboda ba su da bandaki, lamarin da kan zama wata hanya ta yada cutuka a tsakanin jama'a musamman a yankuna na karkara.

A cikin watan Satumba da ya gabata 'yan sanda suka kama wasu mutane biyu a jihar Madhya Pradesh, ta tsakiyar kasar bisa zargin kashe wasu yara 'yan jinsi ko kabilar Dalit, da ke zaman baya-a-dangi a kasar, saboda wai yaran sun yi bahaya a fili.

Mata na shiga hadari saboda tafiya daji domin su yi bahaya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mata a India na shiga hadari saboda tafiya daji domin su yi bahaya

'Yan sandan sun ce mutanen sun rika dukan yaran Roshni, mai shekara 12, da kuma Avinash, mai shekara 10, da sanduna, a lokacin da suke kashin a kusa da titin wani kauye, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar yaran.

Iyaye da dangin yaran sun gaya wa BBC cewa ba su da bandaki a gidansu. A kan irin haka ne mata da yara da dama kan kasance cikin hadari a sanadiyyar zuwa fili ko daji domin su yi bahaya.