Kanin tsohon shugaban kasa zai yi zaman yari na shekara 15

An dauki wannan hoton na Said Bouteflika a shekarar 2012

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An dauki wannan hoton na Said Bouteflika a shekarar 2012, kuma shi din wani babban mai fada a ji ne a zamanin mulkin yayansa Shugaba Abdelaziz Bouteflika
An wallafa

Wata kotun sojin kasar Aljeriya ta yanke wa Said Boutaflika, dan uwan tsohon shugaban kasar hukuncin daurin shekara 15 a gidan yari.

Kotun ta daure shi ne tare da wasu mutum uku da suka hada da wasu tsofaffin jami'an leken asiri biyu da shugaban jam'iyyar 'yan kwadago ta Workers Party.

A watan Mayun da ya wuce ne aka tsare mutum hudun, bayan an shafe makwanni ana wata zanga-zangar da ta tilasta wa Shugaba Boutaflika sauka daga karagar mulki.

Ana dai zarginsu ne da hada baki wajen yin zagon-kasa ga kasarsu da kuma rundunar sojin Algeriya.

An ruwaito cewa kotun ta yi wa tsohon ministan tsaron kasar, Khaled Nizar daurin shekara 20 a bayan idonsa.

Wakilin BBC Ahmed Rouaba ya ruwaito cewa tsohon shugaban kasar, wanda ba shi da lafiya, a yanzu yana zaune ne a wani gida da ke yammacin birnin Algiers, kuma ba a sa ran zai fuskanci shari'a.