Kanin tsohon shugaban kasa zai yi zaman yari na shekara 15

An wallafa

Wata kotun sojin kasar Aljeriya ta yanke wa Said Boutaflika, dan uwan tsohon shugaban kasar hukuncin daurin shekara 15 a gidan yari.

Kotun ta daure shi ne tare da wasu mutum uku da suka hada da wasu tsofaffin jami'an leken asiri biyu da shugaban jam'iyyar 'yan kwadago ta Workers Party.

A watan Mayun da ya wuce ne aka tsare mutum hudun, bayan an shafe makwanni ana wata zanga-zangar da ta tilasta wa Shugaba Boutaflika sauka daga karagar mulki.

Ana dai zarginsu ne da hada baki wajen yin zagon-kasa ga kasarsu da kuma rundunar sojin Algeriya.

An ruwaito cewa kotun ta yi wa tsohon ministan tsaron kasar, Khaled Nizar daurin shekara 20 a bayan idonsa.

Wakilin BBC Ahmed Rouaba ya ruwaito cewa tsohon shugaban kasar, wanda ba shi da lafiya, a yanzu yana zaune ne a wani gida da ke yammacin birnin Algiers, kuma ba a sa ran zai fuskanci shari'a.